
Yayin da Yang Jiechi, ministan harkokin waje na kasar Sin ya ke ganawa da 'yan jarida a jirgin sama bisa hanyar dawowarsa daga Australia zuwa kasar Sin a ran 9 ga wata, ya tattara nasarorin da Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya samu wajen ziyararsa. Ya nuna cewa, ziyarar nan ta samu nasara, kuma ta jawo hankulan kasashen duniya sosai.

Yang Jiechi ya ce, ziyarar wani mihimmin aiki ne da kasar Sin take fuskanta shiyyar Asiya da tekun Pasific a fannin diplomasiya, kuma ta nuna babbar ma'ana wajen sa kaimi ga bunkasuwar dangantaka tsakanin Sin da Australia da kuma zurfafa hadin gwiwa ta shiyyar Asiya da tekun Pasific. Ya ce, lokacin da Mr Hu ya halarci kwarya-kwaryan taro na 15 na shugabannin kungiyar APEC, shugaba Hu Jintao ya bayyana munafofi da ra'ayoyin da gwamnatin kasar Sin za ta bi a kan muhimmin batun da ke shafar moriyar shiyyoyi da duk duniya.(Zainab)
|