 A ran 8 ga wata da yamma, agogon wurin, an bude kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC na karo na 15 da za a shafe kwanaki 2 ana yinsa a birnin Sydney na kasar Australia. A gun taron da aka yi a wannan rana, an zartas da Sanarwar Sydney domin fama da sauye-sauyen yanayin duniya da tabbatar da samar da albarkatun halittu da neman cigaba ba tare da gurbata muhalli ba.
A gun taro na mataki na farko da aka yi domin batun sauye-sauyen yanayin duniya, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya bayar da ra'ayoyi 4 kan yadda za a yi fama da sauye-sauyen yanayin duniya. Mr. Hu ya ce, da farko dai, dole ne a kara yin hadin guiwa a tsakanin kasashe masu arziki da masu tasowa domin fama da wannan matsala. A waje daya, dole ne a tsaya kan matsayin bin hanyar neman cigaba mai dorewa. Bugu da kari kuma, dole ne a fama da sauye-sauyen yanayin duniya a karkashin jagorancin ka'idoji na yarjejeniyar fama da sauye-sauyen yanayin duniya ta M.D.D. da yarjejeniyar Kyoto. Daga karshe dai, Mr. Hu ya ce, dole ne a bi hanyar kirkiro sabbin fasahohi domin karfafa karfin fama da sauye-sauyen yanayin duniya.
Bugu da kari kuma, Mr. Hu ya bayar da shawarar kafa "tsarin gudanar da aikin farfado da gandun daji cikin hali mai dorewa a yankin Asiya da na tekun Pacific".
A wannan rana da yamma, firayin minista John Howard na kasar Australiya ya wakilci bangarorin da suke taron ya sa hannu a kan Yarjejeniyar Sydney. A cikin wannan sanarwa, a bayyane ne an tabbatar da cewa, ya zuwa shekarar 2030, yawan makamashin halittu da ake amfani da shi domin samun kowane GDP a yankin APEC zai ragu da kashi 25 daga cikin kashi dari bisa na shekarar 2005. A waje daya, ya zuwa shekarar 2020, fadin gandun daji da za a shimfida a yankunan APEC zai karu da kadada a kalla miliyan 20. (Sanusi Chen)
|