Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun malam Yakubu Usman, mazaunin birnin Gusau da ke jihar Zamfara, tarayyar Nijeriya. A cikin wata wasikar da malam Yakubu Usman ya turo mana a kwanan baya, ya ce, na san Amurkawa suna bikin nan na "thanksgiving day", shin yaushe ne suka fara yin bikin, kuma me ya sa suke wannan biki?
To, a hakika, bikin "thanksgiving day", ko kuma ranar nuna godiya, wani bikin gargajiya ne da jama'ar Amurka suka fito da shi, haka kuma ranar haduwar iyali ce a gare su, kuma a kan yi wannan biki a ranar Alhamis ta karshe da ke cikin watan Nuwamba na kowace shekara.
Idan muna so mu gano asalin bikin nan na ranar nuna godiya, to dole ne mu bi mafarin tarihin kasar Amurka. A shekarar 1620, shahararren jirgin ruwan da aka fi san shi da sunan "Mayflower" wanda ke dauke da mutanen Ingila 102 ya isa nahiyar Amurka. Sa'an nan, a lokacin hunturu na wancan shekara, wadannan mutanen Ingila 'yan kaka gida sun fada cikin mawuyacin hali, sun yi fama da dari da kuma yunwa. Bayan da lokacin hunturu ya wuce, 50 ne kawai daga cikinsu suka tsira da rayukansu. A lokacin, Indiyawan Amurka masu halin kirki sun kai wa wadannan 'yan kaka gida kayayyakin masarufi da suka wajaba, sun kuma koya musu farauta da kamun kifi da shuka masara da kabewa. Bisa taimakon da suka bayar, wadannan 'yan kaka gida sun sami girbi mai kyau. A ranar murnar samun girbi mai kyau, bisa al'adar gargajiya, 'yan kaka gidan sun bi addininsu, sun tsai da ranar nuna godiya ga ubangiji, sun kuma yanke shawarar gayyatar Indiyawan Amurka zuwa wurin bikin, don nuna musu godiya.
A bikin ranar nuna godiya da aka yi a karo na farko, Indiyawan Amurka da 'yan kaka gida sun hadu a gu daya, sun harba bindiga a alfijir don nuna murna, sa'an nan sun shiga cikin wani daki don nuna godiya ga ubangiji. Daga baya, sun yi kasaitaccen biki. A rana ta biyu da kuma ta uku, sun kuma yi wasan kokawa da tsere da da kuma raye-raye. Sabo da nasarar da aka samu a wajen gudanar da biki na farko na ranar nuna godiya, a cikin shekaru 300 daga baya har zuwa yanzu, ana ci gaba da bin irin wadannan hanyoyi don murnar bikin.
Da farkon fari, babu wani takamaiman lokacin da aka yi wannan biki, sai dai jihohi daban daban suka tsai da lokacin yadda suka ga dama. Kawo shekarar 1863 bayan da kasar Amurka ta sami 'yancin kanta, tsohon shugaba Abraham Lincoln na Amurka ya sanar da bikin a matsayin biki na duk kasar.
Amurkawa sun fi dora muhimmanci a kan abincin dare na ranar nuna godiya. A kasar Amurka, a kan ci abinci kadan a zaman yau da kullum, amma da ranar nuna godiya ta yi, ko wane gida ya kan shirya abinci iri iri, kuma daga cikinsu, talo-talo da wainar kabewa sun zama abincin da ba za a iya rasa su ba. Musamman ma talo-talo, a kan sa abinci iri iri a cikinsa, sa'an nan a gasa shi. Bayan da ya dafu, sai mai gida ya yanke shi, ya rarraba wa kowa. Sabo da haka, ana kuma kiran ranar nuna godiya kamar ranar talo-talo.
A gun bikin murnar ranar nuna godiya, jama'a su kan je coci don yin addu'a da kuma nuna godiya ga ubangiji. Sa'an nan, a kan gudanar da fareti da wasanni iri iri. Yara su kan kwaikwayi Indiyawan Amurka su sa tufafi masu ban mamaki, suna wake-wake da bushe-bushe. A ranar, iyalai su kan hadu a wuri daya, su ci talo-talo.(Lubabatu)
|