Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-07 18:47:57    
An mayar da daidaita sauye-sauyen yanayi a gaban raya tattalin arziki a gun taron koli na kungiyar APEC

cri

Ran 8 zuwa ran 9 ga wata, a birnin Sydney na kasar Australia, an yi kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki a tsakanin kasashen Asiya da tekun Pacifif wato APEC a karo na 15. Shugabanni ko wakilai na mambobi 21 na kungiyar za su halarci wannan taro, wadanda suka hada da shugaba Hu Jintao na kasar Sin, inda za su tattauna sauye-sauyen yanayi da raya kasa ba tare da gurbata muhalli ba da goyon bayan shawarwari na zagaye na Doha da kuma raya tattalin arzikin yankin da suke ciki bai daya da dai sauransu.

Yanzu, a galibi dai ana shimfida kwanciyar hankali a duk duniya da yankin Asiya da tekun Pacific a fannin siyasa, ana kuma bunkasa tattalin arziki ba tare da tangarda ba, ana zurfafa hadin gwiwa a yankuna. Amma ana fuskantar matsalolin tsanantar rashin daiadito a harkokin tattalin arziki da tsanancewar ba da kariyar ciniki da karuwar matsin lamba ta fuskar makamashi da albarkatu da lalacewar muhallin halittu da sauran wadanda ke jawo hankulan mutane. Babban taken kwarya-kwaryar taro na kungiyar APEC da za a yi a wannan karo shi ne 'kara raya yankin Asiya da tekun Pacific bai daya kamar wani iyali, da kuma samar da dauwamammiyar makoma tare'. A lokacin taro, shugabannin za su tattauna batutuwa daban daban bisa matakai 2. Za a tattauna batun sauye-sauyen yanayi a taro na mataki na farko, za a yi tattaunawa kan sauran batutuwa a taro na mataki na biyu.

Muhimman dalilan da suka sa batun sauye-sauyen yanayi ya jawo hankalin kungiyar APEC sosai shi ne domin da farko, a 'yan kwanakin da suka wuce, kwamitin musamman kula da sauye-sauyen yanayi a tsakanin gwamnatoci na Majalisar Dinkin Duniya wato IPCC da hukumar kula da yanayi ta kasa da kasa da hukumar tsara shiri kan kiyaye muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya suka kafa cikin hadin gwiwa ya gabatar da rahoton kimantawa a karo na 4. Wannan rahoto na da muhimmanci sosai wajen jagorantar bangarori daban daban da su tsai da kuduri. Ban da wannan kuma, 'yarjejeniyar Kyoto' da aka tsara wa kasashe masu sukuni ma'aunin rage fitar da abubuwan da ke gurbata muhalli za ta cika wa'adin aikinta a shekarar 2012. Yanzu an kaddamar da shawarwari kan 'yarjejeniyar Kyoto ta nan gaba' don tabbatar da ka'idojin da bangarorin daban daban za su bi wajen rage fitar da iska mai dumamar yanayi bayan shekarar 2012. Shi ya sa yanzu kasashen duniya da ke kunshe da kungiyar APEC suna bukatar tattauna wannan batu cikin himma.

Na biyu kuma, yanzu yana kasancewa da sabani a tsakanin bangarori daban daban da kuma rukunonin daban daban kan yadda za su daidaita batun sauye-sauyen yanayi, shi ya sa ana bukatar kara yin cudanya da tattaunawa kan wannan muhimmin batu don samun ra'ayi daya. An kiyasta cewa, a gun wannan taron koli, dukkan mambobin kungiyar za su yi tattaunawa cikin kwazo, sa'an nan kuma, za su daddale da kuma gabatar da 'sanarwar Sydney' game da sauye-sauyen yanayi.

A gun wannan taron koli, batun da ke shafar goyon bayan shwarwari na zagaye na Doha ya kuma jawo hankulan mutane sosai. Ra'ayi daya da mambobin kungiyar APEC za su samu yana da matukar muhimmanci ga shawarwari na zagaye na Doha, wadanda yawan kudaden da suka samu daga ciniki ya wuce rabin wadanda kasashen duniya suka samu daga ciniki. Ran 3 ga wata, a Sydney, shugaba David Spencer na taron manyan jami'ai na shekarar 2007 na kungiyar APEC ya ce, shugabannin mambobin kungiyar mahalarta taron za su ba da sanarwa, inda za su yi alkawarin sa kaimi kan shawarwari na zagaye na Doha cikin himma don neman shiga shawarwari na mataki na karshe kafin karshen wannan shekara.

Dadin dadawa kuma, mambobin kungiyar APEC sun kammala nazarin bunkasa tattalin arzikin yankin da suke ciki gu daya, sun sami sabon ci gaba a fannin yin hadin gwiwar ciniki da zuba jari, sun kara yin cudanya da rukunin masana'antu da kasuwanci a bayyane. An kiyasta cewa, taron koli da za a yi a wannan karo zai zartas da 'rahoto kan bunkasa tattalin arzikin yankin Asiya da tekun Pacific gu daya' da amincewa da shawara da manufa kan sa kaimi kan bunkasa tattalin arzikin yankin gu daya don zabura aikin bunkasa tattalin arzikin yankin gu daya.

Manazarta sun yi hasashen cewa, wannan taron koli zai ba da taimako ga dukkan mambobin kungiyar wajen kara yin cudanya da tattaunawa kan batutuwa da yawa, da samar da kyakkyawan makoma wajen yin hadin gwiwa a tsakaninsu, ban da wannan kuma, zai ba da taimako wajen tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwar yankin Asiya da tekun Pacific.(Tasallah)