Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-07 18:47:45    
Shugaba Hu Jintao ya gana da shugabannin kasashen Korea ta kudu, da New Zealand, da Peru da kuma Papua New Guinea

cri

Ran 7 ga wata a birnin Sydney, bi da bi ne shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya gana da shugaba Roh Moo Hyun na kasar Korea ta kudu, da firaminista Helen Clark ta kasar New Zealand, da shugaba Alan Garcia Perez na kasar Peru, da firaminista Somare na kasar Papua New Guinea.

Yayin da Mr. Hu ya gana da Mr. Roh Moo Hyun, ya ce, a karkashin kokarin da bangarorin dabam daban suka yi, shawarwarin tsakanin bangarori shida sun sami cigaba, kasar Sin tana son cigaba da sa kaimi ga yankuri na wannan shawarwari yadda ya kamata domin sanya tsibirin Korea ya zama wani yanki da babu makaman nukiliya a ciki cikin sauri. Mr. Roh Moo Hyun ya ce, kasar Sin ta ba da gudumawa sosai wajen sa kaimi ga yunkurin shawarwarin tsakanin bangarori shida.

Yayin da Mr. Hu ya gana da Madam Clark, inda ya nuna cewa, kullum kasar Sin tana mai da hankalinta bisa manyan tsare tsare kan huldar da ke tsakanin kasashen Sin da New Zealand, shawarwari kan 'yancin cinikayya da ke tsakanin kasashen biyu yana da babbar ma'anar tarihi. Madam Clark ta ce, ana yin shawarwari kan 'yancin cinikayya yadda ya kamata, wannan zai karfafa huldar da ke tsakanin kasashen biyu.

Ban da haka kuma, bi da bi ne Mr. Hu ya gana da shugaba Alan Garcia Perez na kasar Peru da firaminista Somare na kasar Papua New Guinea, inda ya nuna godiya ga kasashen biyu saboda kullum suna tsaya tsayin daka kan ka'idar kasar Sin daya tak a duniya.