Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-07 17:51:43    
Cibiyar wasannin motsa jiki ta Qinhuangdao

cri

Aminai 'yan Afrika, a cikin shirinmu na kwanan baya dai, mun dan gutsura muku wani bayani a game da makarantgar wasan kwallon kafa ta Qinhuangdao. Yau dai, za mu kawo muku wani bayani kan cibiyar wasannin motsa jiki ta Qinhuangdao. Tuni a watan Yuli na shekarar 2004 ne aka kammala gina wannan cibiya da kuma soma amfani da ita a hukumance, wadda kuma ta kasance wani babban filin wasan motsa jiki na farko da aka somagina shi da yin afmani da shi bayan da aka kammala gina shi dake cikin rassan filayen wasa na gasannin kwallon kafa na taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008.

Cibiyar wasannin motsa jiki ta Qinhuangdao tana a bakin teku a unguwar Haigang ta birnin Qinhuangdao. Fadin ginin cibiyar ta kai murabba'in-mita 74,600; kuma jimlar kudin da aka kashe wajen gina ta ta kai kudin Sin wato RMB Yuan miliyan 150. Wannan cibiyar wasannin motsa jiki na iya daukar 'yan kallo kimanin 30,000. Abu mai sha'awa shi ne, idan an duba ginin cibiyar mai hawa shida daga can nesa, to za a iya ganin cewa siffar ginin tana kama da wani kwale-kwale dake tafiya kan teku.

1 2