Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-07 17:00:18    
Shugaban Hu Jintao ya gana da takwarorinsa na kasashen Korea ta kudu da Peru da Papua New Guinea

cri

Ran 7 ga wata a birnin Sydney, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gana da shugabannin kasashen Korea ta kudu da Peru da firayim ministan kasar Papua New Guinea Michael Somare, wadanda suka halarci kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar hadin kan tattalin arziki na Asiya da yankunan tekun Pasific wato kungiyar APEC a wurin.

A gun ganawa, shugaban Hu Jintao ya bayyana cewa, bisa kokarin da aka yi, shawarwari tsakanin bangarori 6 ya sami kyakkyawar bunkasuwa, wanda zai aza tushe mai inganci ga ayyukan da za a yi gaba. Bangaren Sin yana son ba da gudummowarsa tare da bangarori daban daban da abin ya shafa ciki har da Korea ta kudu duk domin ciyar da shawarwarin tsakanin bangarori 6 gaba, da kuma cimma burin tabbatar da rashin kasancewar makaman nukiliya a zirin Korea tun da wuri.

Shugaban kasar Korea ta kudu Roh Moo-hyun ya bayyana cewa, shawarwari shi ne hanyar mafi kyau don warware batun makaman nukiliya a zirin Korea. A matsayin kasar dake shugabantar taron, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa don cigaban shawarwarin cikin lumana.

Yayin da ya gana da shugaban Peru Alan Garcia Perez, shugaba Hu Jintao ya ce, kasar Peru kasa daya ce dake cikin kasashen Latin Amurka da suka kulla dangantakar diplomasiyya da kasar Sin tun da farko. Ingiza kuma bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen 2 ya dacewa da moriyar kasashen 2 da na jama'arsu, kuma ya kawo amfani ga zaman lafiya da bunkasuwa na yankuna da duniya. Kazakila ma Mr. Garcia ya bayyana cewa, Peru ta tsaya tsayin daka kan matsayin Sin daya tak a duniya, wanda ya kasance ka'idar da dukkanin kasashen duniya suka bi. Mr. Hu Jintao ya nuna yabo sosai kan wannan.

Lokacin da shugaba Hu ya gana da firayim ministan Papua New Guinea Mr. Somare ya yi nuni da cewa, Papua New Guinea aboki mafi muhimmi ne wajen hadin kan tattalin arziki gare Sin a tsibirorin dake tekun Pasific, kuma kasar Sin za ta goyi bayan rayuwar kasar kamar ta saba yi a da. Mr. Kuma Somare ya ce, Papua New Guinea tana goyon bayan matsayin da Sin ta dauka kan batun Taiwan ba tare da kasala ba. Hu Jintao shi ma ya nuna babban yabo kan wannan.

Ban da haka, ran nan a birnin Sydney, shugaba Hu Jintao ya gana da shugaban jam'iyyar 'Labor Party' ta kasar Australia Kevin Rudd, inda ya nuna cewa, bangaren Sin zai daidaita dangantakar tsakanin Sin da Australia bisa hangen nesa, kuma za ta hada hai da bangarori daban daban na Australia domin yunkurin daga matsayin hadin gwiwa tsakaninsu zuwa wani sabon mataki.(Salmatu)