Mataimakin shugaban kungiyar hadin kan masana'antun kera injuna na kasar Sin Zhang Xiaoyu ya bayyana a ran 7 ga wata cewa, a shekarar 2007, an kiyasta cewa, yawan motocin da kasar Sin ta kera ta kuma sayar da su za su wuce miliyan 9.
Mr Zhang ya yi wannan kiyasi ne a gun taron shekara-shekara na ayyukan motocin kasar Sin na shekarar 2007 wanda aka shirya a birnin Tianjin dake arewacin kasar Sin.
Ya ce, yawan motocin da aka kera ya sami karuwa da sauri cikin shekaru 6 a jere da suke wuce, daga shekarar 2001 zuwa shekarar 2006, matsakaicin yawan karuwar motocin da aka kera a kowace shekara ya kai kashi 26 cikin dari. A shekarar 2006, yawan motocin da kasar Sin ta kera ta kuma sayar da su dukansu sun wuce miliyan 7.2, kasar Sin tana biye da kasar Amurka, wato ke nan ta riga ta kama matsayi na 2 a duniya wajen kasancewa wata kasuwa mafi girma don sayar da sabbin motoci.(Lami)
|