Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-06 21:23:42    
Shugaba Hu Jintao ya gana da takwaransa na kasar Amurka

cri

A ran 6 ga wata, a birnin Sydney, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya gana da takwaransa na kasar Amurka George W. Bush da ya zo birnin don halartar kwarya-kwaryar taro na 15 na shugabannin kasashe membobin kungiyar APEC, inda bangarorin biyu suka yi musanyar ra'ayoyinsu kan tattalin arzikin da cinikayya tsakaninsu da batun Taiwan da sauye-sauyen yanayi da dai sauran al'amuran duniya da na shiyya-shiyya da ke jawo hankulansu.

Shugaba Hu ya nuna cewa, yanzu, halin da duniya ke ciki yana samun sauye-sauye sosai, bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka lami lafiya ba kawai ya dace da babbar moriyar kasashen biyu ba, har ma zai ba da taimako wajen zaman lafiya da bunkasuwar duk duniya. Bangaren Sin yana son yin kokari tare da Amurka domin tabbatar da ciyar da dangantakar hadin gwiwa tsakaninsu zuwa gaba.

Shugaba Bush ya bayyana cewa, kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka zai taka muhimmiyar rawa ga kasashen biyu, Amurka da Sin muhimman kasashe biyu ne na duniya, inganta hadin kansu zai iya warware matsaloli da yawa.

Game da batun Taiwan, shugaba Hu ya jaddada cewa, dole ne mu yi wa hukumar Taiwan gargadi mai tsanani, cewa yunkurin neman 'yancin kan Taiwan da ake yi ta ko wace irin hanya ba zai samu nasara ba.

A nasa bangaren kuma shugaba Bush ya nanata cewa, kasar Amurka tana tsayawa tsayin daka kan kasar Sin daya tak a duniya, tana bin hadaddun sanarwa uku da ke tsakanin Amurka da Sin, kuma za ta ki amincewa da ko wace harkar da wani bangare zai yi don canja halin da mashigin tekun Taiwan ke ciki yanzu.(Kande Gao)