A ran 6 ga wata da yamma, agogon wurin, an shirya bikin kaddamar da taron koli na kasuwanci na kungiyar APEC da za a shafe kwanaki biyu ana yinsa a dakin wasan kwaikwayo na birnin Sydney na kasar Australiya. A gun taron, shugabannin membobin kungiyar APEC da 'yan kasuwa za su yi tattaunawa kan batutuwan shiyya-shiyya da ke jawo hankulansu, ciki har da na tattalin arziki da cinikayya da albarkatun halittu da muhalli da sauye-sauyen yanayi domin neman hanyoyin warware su. Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya halarci bikin kaddamar da wannan taro, kuma ya bayar da wani jawabi mai lakabi haka: "Kara yin hadin guiwa daga duk fannoni domin neman cimma dawaumammen cigaba". A cikin jawabinsa, ya bayar da matsayin da kasar Sin take dauka kan maganganun tattalin arziki na duniya da na shiyyar Asiya da na tekun Pacific da suke jawo hankulan mutane sosai.
Yanzu, tattalin arzikin duniya yana samun sauye-sauye sosai. lokacin da dama da kalubale suna kasancewa tare, yaya za a yi hadin guiwa domin neman samun dawaumammen cigaba tare ya zama wata matsala mai tsanani da ke kasancewa a gaban duniya. Sabo da haka, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya bayar da ra'ayoyi 5. Mr. Hu ya ce, "Da farko dai, neman cigaban tattalin arzikin duniya cikin halin daidaito muhimmin tushe ne ga kokarin neman samun dawaumammen cigaba. Sannan, kafa tsarin kasuwanci a tsakanin bangarori daban-daban kamar yadda ya kamata muhimmin abu ne wajen tabbatar da samun dawaumammen cigaba. Haka kuma, samar da albarkatun halittu cikin hali mai dorewa muhimmin abu ne da ke neman samun dawaumammen cigaba. Bugu da kari kuma, kiyaye muhallin da muke ciki, muhimmin sharadi ne ga kokarin cimma dawaumammen cigaba. Daga karshe dai, raya da kirkiro sabbin fasahohin zamani da ilmi muhimmin karfi ne wajen neman samun dawaumammen cigaba. "
A waje daya, Mr. Hu ya bayyana wa mahalarta taron fifiko da kasar Sin ta samu a cikin shekaru 29 da suka gabata bayan da ta aiwatar da manufofin yin gyare-gyare da bude kofa kuma muhimmiyar rawar da take takawa tattalin arzikin duniya. Mr. Hu ya ce, abubuwan a-zo-a-gani sun shaida cewa, cigaban da tattalin arzikin kasar Sin ke samu cikin hali mai dorewa ba ma kawai yana moriyar Sinawa biliyan 1.3 ba, har ma yana samar wa sauran kasashen duniya damar yin kasuwanci sosai da sa kaimi kan cigaban tattalin arzikin duniya. Ya jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da taka rawarta wajen neman samun dawaumammen cigaban duniya. Ya ce, "Kasar Sin za ta ci gaba da bin sabuwar hanyar raya masana'antu wadda take kunshe da fasahohin zamani da ilmin kimiyya, kuma za a iya yin tsimin makamashin halittu da rage fitar da yawan abubuwa masu gurbata muhalli, kuma 'yan kwadago za su iya bayar da gudummowarsu yadda ya kamata lokacin da ake samun moriyar tattalin arziki."
A cikin 'yan watannin nan da suka gabata, wasu kafofin watsa labaru na duniya suna shakkar ingancin kayayyaki da abinci na kasar Sin. Sabo da haka, a cikin jawabinsa, Mr. Hu ya bayyana matsayi da ra'ayoyin da bangaren kasar Sin yake dauka. Ya ce, "Kasar Sin tana mai da hankali sosai kan ingancin kayayyaki da abincin da ake fitar da su zuwa kasashen waje. Tana aiwatar da dokoki iri iri lokacin da take sa ido kan ingancinsu yayin da ake yinsu da sufurinsu da shigi da ficinsu. Muna sauke nauyin da ke bisa wuyanmu kamar yadda ya kamata, kuma muna namijin kokari domin tabbatar da ingancin kayayyaki da abinci."
A cikin nasa jawabin, daga karshe dai, Mr. Hu Jintao ya bayyana cewa, neman samun cigaba tare dalili da buri ne da suka sa kasar Sin ta shiga kungiyar APEC. Mr. Hu ya ce, "Idan mu yi amfani da dama da kara yin hadin guiwa a tsakaninmu kamar yadda iyalai suke neman bunkasuwa tare, ko shakka babu, za a iya samun dawaumammen cigaba a shiyyar Asiya da ta tekun Pacific gaba daya." (Sanusi Chen)
|