Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-06 17:23:51    
"Hanyar ruwan zinariya" wato kogin Yangtze na kasar Sin

cri

Tun lokacin aiwatar da "shirin na 9 na shekaru 5-5 na raya kasa" wato daga shirin "shekara ta 1996 zuwa ta 2000" zuwa yanzu, kasar Sin ta kara ware kudi da yawa domin gyara kogin Yangtze, ta yadda wannan "hanyar ruwan zinariya" tana ta kawo amfani ga sufurin jiragen ruwa.

Babbar hanyar jiragen ruwa ta kogin Yangtze ta tashi daga birnin Shuifu na lardin Yunnan da ke kudancin kasar Sin ta malala har zuwa birnin Liuhekou na lardin Jiangsu da ke gabashin kasar, duk tsawonta ya kai kilomita 2838, kashi 95 bisa 100 na wannan hanyar tana da sharuda masu kyau wajen halitta. A farkon lokacin aiwatar da "shirin na 9 na shekaru 5-5 na raya kasa", majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta nemi hanyar jiragen ruwa ta kogin Yangtze da ta zama ginshiki ga yin zirga-zirgar jiragen wuwa a shiyyar mashigar kogin Yangtze a teku.

A shekarar 2003 ma'aikatar zirga-zirga ta kasar Sin ta yarda da shirin "bunkasa muhimmiyar hanyar jiragen ruwa ta kogin Yangtze" wanda a ciki aka gabatar da cewa ya kamata a zurfafa ruwan kogin Yangtze a kuriyar kogin, da yin zirga-zirgar jiragen ruwa cikin sauki a sashen tsakiya, da kuma kara tsawon hanyar ruwan kogin a mafarinsa.

Domin cim ma wannan manufa, an yi aikin kyautata tsarin hanyar zirga-zirgar jiragen ruwa ta kogin Yangtze, ta yadda zurfin ruwan kogin ya karu har ya kai mita 10 daga mashigar kogin Yangtze a teku zuwa birnin Nanjing. Wannan ya ba da sharuda domin zirga-zirgar jiragen ruwa cikin sauki sosai.

Domin kara ba da jagora ga hanyar jirgin ruwa da, hukumar kula da hanyar zirga-zirgar jiragen ruwa ta kogin Yangtze ta yi wasu ayyukan gine-gine masu ba da taimako ga sashen kogin da ke tsakanin birnin Nanjing da na Liuhekou, kuma an tabbatar da manufar samun babbar alamar da ke nuna hanyar jirgin ruwa, da kafa fitilu masu ba da haske sosai, da yin gine-gine na zamani domin ba da taimako ga zirga-zirgar jirgen ruwa, sabo da haka an biya bukatar yin zirga-zirgar manyan jiragen ruwa na zamani a sashen kogin daga birnin Nanjing zuwa mashigar kogin Yangtze a teku.

Gine-ginen zamanin da aka yi a kuriyar kogin Yangtze sun kawo babbar moriyar tattalin arziki da zaman al'umma ga sha'anin zirga-zirgar jiragen ruwa da shiyyoyin da ke bakin kogin. Bisa kididdigar da hukumar harkokin teku ta lardin Jiangsu ta yi an ce, cikin shekara daya na bayan aikin yasa yashi a sashen kogin Yangtze na daga birnin Nanjing zuwa Liuhekou, yawan hadarurrukan jiragen ruwan da suka faru a wannan sashen kogin ya ragu da kashi 42.1 cikin 100 bisa na kafin an yi wannan aiki, yawan mutanen da suka mutu sabo da hadarin jirgin ruwa kuma ya ragu da kashi 46 bisa 100, yawan hasarar da aka samu wajen tattalin arziki kuma ya ragu da kashi 45.4 bisa 100, wato yawan GDP da aka samu ya karu da kudin Renminbi Yuan biliyan 54.

Bayan gine-ginen da aka yi domin kyautata hanyar jirgin ruwa, wannan "Hanyar ruwan zinariya" wato kogin Yangtze na kasar Sin tana nan tana zama muhimmin ginshiki wajen bunkasa tattalin arziki da sana'o'in da ke kwarin kogin. Yanzu, yawan karafan da aka narke a kwarin kogin Yangtze ya kai kashi 36 cikin 100 bisa na duk kasar Sin, yawan kayayyakin man fetur da aka fitar ya kai kashi 28 cikin 100 bisa na duk kasar, yawan motocin da aka kera kuma ya kai kashi 47 cikin 100 bisa na duk kasar.

Abun da ya kamata a jaddada a kai shi ne, wannan "Hanyar ruwan zinariya" wato kogin Yangtze na kasar Sin ta zama muhimmin albarkatun da ya tabbatar da rinka samun ci gaban tattalin arziki mai dorewa a kwarin kogin.