Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-06 16:48:18    
Taron ministoci na kungiyar APEC ya yi kira da a ingiza yunkurin shawarwarin zagaye na Doha

cri

An rufe taron ministoci na karo na 19 na Kungiyar hada kan tattalin arzikin yankunan Asiya da na tekun Pacific a ran 6 ga wata a birnin Sydney. Taron ya bayar da wata sanarwar hadin gwiwa cewa, ya yi kira da a ingiza yunkurin shawarwarin Doha, da gaggauta bunkasa shiyya-shiyya bai daya ta hanyar yin gyare-gyare wajen ciniki da tattalin arziki, da karfafa ayyukan ba da tabbaci ga tsaron dan Adam na yankunan Asiya da na tekun Pacific, da kuma ci gaba da yin kwaskwarimar hukumomin kungiyar APEC.

Ministan harkokin wajen kasar Sin Yang Jiechi da ministan kasuwancin kasar Sin Bo Xilai sun yi jawabi a gun taron, inda suka bayyana matsayin da bangaren Sin ya dauka kan manyan batutuwan da za a tattauna a kai.

An fara wannan taron ne daga ran 5 ga wata a birnin Sydney. A cikin kwanaki 2 da aka yinsa, wakilan kasashe membobi guda 21 sun yi tattaunawa sosai kan batun goyon baya ga shwarwarin zagaye na Doha na APEC da yunkurin bunkasa shiyya-shiyya bai daya da tsaron dan Adam da sauyin yanayi da samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba da kuma yin gyare-gyare a cikin kungiyar APEC da sauran batutuwa, sun yi wannan tattaunawa ne bisa jigon "kara gina babban iyali don samun dauwamammiyar makoma tare".(Lami)