A ran 5 ga wata a birnin Sydney, Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya gana da Morris Iemma, gwamnan jihar New South Wales ta kasar Australia.
Mr Hu ya nuna cewa, a cikin shekarun da suka wuce, an samu bunkasuwa mai zurfi kan zumunci da hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da jihar New South Wales. Gwamnatin kasar Sin ta dora muhimmanci kan raya dangantakar sada zumunci da hadin gwiwa tsakanin su, kuma tana fatan yin kokari tare da gwamnatin jihar New South Wales da bangarori daban daban wajen samo sabin hanyoyin bunkasuwa da sa kaimi ga bunkasuwar hadin gwiwa da moriyar juna a fannonin tattalin arziki da cinikayya da kimiyya da fasaha da ilmi da kiyaye muhalli da yawon shakatawa.
Mr Iemma ya bayyana cewa, a cikin shekaru 35 da suka wuce, ga jihar New South Wales, dangantakar sada zumunci tsakanin Sin da jihar ta taka muhimmiyar rawa, kuma ta kawo wa jihar al'adu iri daban daban da wadatattun tattalin arziki. Jihar New South Wales tana fatan za a samu nasarori masu dimbin yawa wajen hadin gwiwarsu.
Mr Hu ya sauka a Sydney ne a ran 5 ga wata da yamma. Yayin da shugaba Hu Jintao ke ziyara a birnin Sydney, Mr Hu zai yi shawarwari tare da firayin minista David Hawker. Daga baya kuma shugaba Hu zai halarci taron shugabannin kungiyar hadin gwiwa kan tattalin arziki a shiyyar Asiya da tekun Pacific da za a yi ba a hukunce ba, kuma taron shawarwari tsakanin shugabanni da wakilan majalisar ba da shawara kan masana'antu da cinikayya na kungiyar hadin gwiwa kan tattalin arziki a shiyyar Asiya da tekun Pacific da taron koli na cinikayya na kungiyar hadin gwiwa kan tattalin arziki a shiyyar Asiya da tekun Pacific.(Zainab)
|