Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-06 14:39:48    
Kasar India ta kara saurin bunkasa man fetur a Afrika

cri
Bisa bunkasuwar matakin tattalin arziki da ta samu, kasar India tana ta kara bukatar makamashi a kwana a tashi. Amma, sabo da kasar India tana karancin makamashi a cikin kasar, don haka, ta kashe kudade da yawa a ko wace shekara, domin shigar da man fetur da gas, haka kuma batun makamashi ya zama wata muhimmiyar matsalar da ke hana bunkasuwar tattalin arziki ta kasar India. Tun daga shekarar 2005, a lokacin da kasar India ta ke yin safiyo a Latin Amurka, da Asiya, da Turai, da kuma sauran shiyyoyi, a waje daya kuma ta kara saurin bunkasa man fetur a Afrika.

A takaice dai, kasar India wata kasa ce mai karancin man fetur, gas da aka ajiye a kasar kuma ba su da yawa. Bisa rahoton kididdigar makamashin duniya da kamfanin man fetur na kasar Ingila da ya fi girma wajen samar da makamashi a duk duniya ya bayar ba da dadewa ba, an ce, ya zuwa karshen shekarar 2006, yawan adanannen man fetur da kasar India ta gano ya kai ganguna biliyan 5.7, wato ya karu da ganguna miliyan 900 bisa na shekaru biyar da suka wuce. Rahoton ya nuna cewa, yawan man fetur da kasar India ta fitar a ko wace rana ya kai ganguna dubu 807, bisa saurin fitar da man fetur na yanzu, kasar India za ta haka duk adanannen man fetur da ta gano a cikin shekaru 19.3 masu zuwa.

Yanzu, kasar India ta zama wata babbar kasa mai sayen man fetur a duniya. Sabo da ba ta da isasshen man fetur a cikin kasar, don haka kashi 75 cikin dari na man fetur da take bukata sun fito ne daga kasashen waje. Hukumar makamashi ta duniya ta kimanta cewa, ya zuwa shekarar 2030, yawan man fetur da kasar India za ta shigar da shi zai kai kashi 90 cikin dari bisa na man fetur da take bukatar.

Shigar da yawan man fetur mai tsada, ta kara nauyin da ke bisa wuyan kasar India wajen tattalin arziki da sha'anin kudi. Wani jami'in ma'aikatar sha'anin kudi ta kasar ya nuna cewa, idan farashin man fetur na duniya ya karu da dollar Amurka 5 na ko wane ganga, to saurin karuwar yawan kudin da aka samu daga wajen aikin kawo albarka a cikin gida zai ragu da kashi 0.5 cikin dari. Domin biyan bukatunta na samun bunkasuwar tattalin arziki, kasar India ta kara karfin yin safiyo da raya makamashin man fetur a Afrika.

Kamfannonin man fetur da gas na gwamnatin kasar India sun cimma yarjejeniyoyi tare da hukumomin da abin da ya shafa na kasar Nijeriya, wato kasar da ta fi girma wajen fitar da man fetur a Afrika. A sakamakon haka, kasar India ta samu ikon bunkasa wurarren da ke da adanannen man fetur a cikin ruwa mai zurfi guda biyu na kasar Nijeriya a cikin shekaru 25 masu zuwa. Yawan man fetur da ake fitar da su a ko wace rana na wadannan wurarren adannen mai biyu ya kai kimanin ganguna dubu 650. Domin saka wa Nijeriya alherin da ta yi mata, kasar India za ta zuba jari na dollar Amurka biliyan 6 kan manyan ayyukan kasar a fannonin samar da wutar lantarki, da hanyoyin jiragen kasa, da sha'anin noma, da dai sauransu.

A kasar Ghabon da ke tsakiyar Afrika, wasu kamfannonin man fetur da na gas na kasar India sun cimma yarjejeniyoyin raya man fetur tare da gwamnatin kasar Ghabon a watan Nuvamba na shekarar 2005, a sanadiyar haka, wadannan kamfannoni sun samu amincewa wajen yin safiyo da raya filin man fetur na Shakthi. Wannan filin man fetur yana shiyyar fadama da ke tsakiyar kasar Ghabon, fadin muraba'insa ya kai kilomita 3761.

A kasar Sudan da ta fi fadin muraba'i a Afrika kuma, yawan kudin da kasar India ta zuba wajen yin safiyo da raya man fetur ya wuce dollar Amurka biliyan 1.5. Bisa rahoton da hukumar tattara bayanai game da makamashi ta kasar Amurka ta bayar, an ce, ya zuwa yanzu, yawan man fetur da aka haka a kasar Sudan ya kai kamar ganguna biliyan daya kawai, don haka, kasar India tana mayar da aikin haka man fetur a kasar Sudan da ya zama muhimmin fanni wajen zuba jari.

Bayan haka kuma, kasar India tana da ayyukan yin safiyo da raya man fetur a kasashen Libya, da Angola, da dai sauransu.