Ran 5 ga wata da yamma, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya sauka a birnin Sydney domin cigaba da yin ziyarar aiki a kasar Australiya, kuma zai halarci kwarya-kwaryar taron koli na karo na 15 na kungiyar APEC da za a bude a wannan birni.
Yayin da shugaba Hu Jintao ke yin ziyara a birnin Sydney, zai yi shawarwari tare da firaminista Howard, kuma zai halarci kwarya-kwaryar taron koli na kungiyar APEC, da taron shawarwari tsakanin shugabanni da wakilan kwamitin kula da harkokin masana'antu da kasuwanni, da taron koli na kasuwanci na kungiyar APEC. Shugaba Hu Jintao zai bayyana matsayin kasar Sin kan yunkurin hadin guiwia ta kungiyar APEC, da sauyawar yanayi, da manyan matsalolin da ake fuskanta wajen bunkasa tattalin arziki.
A ran 5 ga wata da safe a birnin Canberra, shugaba Hu Jintao ya gana da Mr. Hawker shugaban majalisar dokoki da Mr. Ferguson shugaban majalisar dattijai ta kasar Australiya. Shugaba Hu Jintao ya ce, huldar da ke tsakanin kasashen Sin da Australiya tana cikin zamani mafi kyau a tarihi. Amincewar da ke tsakanin kasashen biyu tana ta karuwa kan siyasa, kuma cudanyar da ke tsakanin hukumomin kafa dokoki na kasashen biyu ta sami cigaba sosai.
|