Kwanan baya, a dakalin nuna wasannin fasha na birnin Beijing, an nuna wasannin kwaikwayo da ke hada da raye-raye da wake-wake na kabilar Tibet, a cikinsu da akwai wata wasan kwakwayo da ke da lakabi haka: Garinmu da ke jawo wa mutane mamaki. An taba nuna wasan nan a kasashen Dermark da Italiya da Korea ta kudu da Austria da sauransu .
wasan nan na kabilar Tibet da ke da lakabi "Garinmu da ke jawo wa mutane mamaki ya bayyana halin da ake ciki tamkar yadda abubuwan da aka tanada a cikin rubutattun wakokin . A cikin wasan, an bayyana yadda wata budurwa mai suna Qu Ni tare da sauran mutanen iyalansu guda uku suke zaman rayuwa na yau da kullum a gabashin jihar Tibet ta kasar Sin da yadda 'yan kabilar Tibet suke aikin wurjanjan da kuma yadda samari maza da mata suke shiga soyayya a tsakaninsu da yin murnar bikin aure da bikin haihuwa da sauran al'adar gargajiya ta kabilar Tibet. 'Yan kabilar Tibet suna nuna kaunarsu ga rana da rayukka da yankunan kasa , kuma suna girmama halittu, dukan karfinsu da tausayinsu suna bayyanuwa sosai a cikin wake-wake da raye-raye da 'yan wasa na kabilar Tibet suka yi.
tare da wake-waken zamanin yau da aka yi cikin faranta rai sosai ne, 'yan wasan da ke sanye da tufaffin kabilar Tibet da suka zo daga birnin Changdu na jihar Tibet suna rawa bisa al'adar gargajiyarsu, wani lokaci, suna juyawar jikinsu, wani lokaci kuma, suna tsalle-tsalle tare da isowarsu da farin ciki, kai, wasan nan ya burge 'yan kallo sosai da sosai.
Wata 'yar kallo ta bayyana cewa, 'yan wasan suna nuna wasanni cikin halin jan zuciya sosai, duk saboda su ne 'yan kabilar Tibet da ke da karfin kuzari sosai, ga dukan abubuwan zane-zanen da aka yi a kan dakalin nuna wasanni, da akwai karamin gargadan da ke ketare gangarar duwatsu, kai, su ne abubuwan da muke tsammanin tamkar yadda jihar Tibet da muke ciki , a gaskiya dai dukan abubuwan da aka yi na gargajiya ne kawai, sun bayyana abubuwan mamaki sosai, a cikin zuciyarmu, wasannin da aka yi tamkar yadda muke cikin wata duniya mai ban mamaki sosai, muna begen wurin, muna son sa kafarmu a wurin.
Jihar Tibet da ke yammacin kasar Sin tana kan wurin da ke da mita dubu 40 ko fiye daga leburin teku, ana kan kiranta da cewar wai kololuwar duniya. A jihar tibet, da akwai kokuwa mafi tsayi a duniya, wato kokuwar Himalaya tare da babban kwari mafi zurfi a duniya, wato babban kwari da kogin Yaluzangbu ke malala. A jihar Tibet, ba a iya samun isasshen iska ba, amma hasken rana na da yawan gaske tare da kurmi da ruwan ido mai zafi da korama da tafki a kan manyan tsaunukan da ke rufewar kankara mai taushi ko ciyayi masu kore shur da tsire-tsire da dabbobi da ba a iya samunsu a sauran wurare ba. Jihar Tibet ita ce inda ake somar al'adun kabilar Tibet, jihar Tibet jiha ce mai ban mamaki da mutane suke begen sa kafa a ciki.
A jihar Tibet, ana rawa sosai, musamman ma akwai manyan rawaye irinsu guda uku, yanzu kasar Sin ta riga ta maido da su tamkar yadda abubuwan tarihi ba na kayayyaki ba. Wadda ke nuna wasan da ke da lakabi "garinmu da ke jawo wa mutane mamaki" ita ce kungiyar wake-wake da raye?raya ta birnin Xichang na jihar Tibet. Kungiyar tana da tarihi da yawan shekarunta ya kai 34, dukan mambobin kungiyar su ne mutanen kabilar Tibet kawai, wani lokacin da suke nuna wasanni, sai sanyawar rigunansu na irin kabilar Tibet kawai suke yi. Shugaban kungiyar ta yi farin ciki da gai da masu sauraron gida rediyo kasar Sin da harshen Tibet cewa, sannu , aminanmu! Mun sa ran alheri gare ku.
Ya ce, a kowace shekara, suna nuna wasanni sau 50 a duk fadin kasar Sin ko a duniya, suna yin gadon gargajiya, suna ta kara kagowar sabbin wasanni, suna yadada fasahohin kabilar Tibet sosai.(Halima)
|