Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-05 16:52:12    
Shugaban Kasar Sin Hu Jintao ya gana da shugaban majalisar dokokin kasar Australia David Hawker da shugaban majalisar dattijan kasar Alan Ferguson

cri
A ran 5 ga wata, a birnin Canberra, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gana da shugaban majalisar dokokin Australia David Hawker da shugaban majalisar dattijan kasar Alan Ferguson.

Mr. Hu Jintao ya ce, amincewar juna a fannin siyasa tsakanin bangarorin Sin da na Australia tana ci gaba da karuwa, sakamakon da suka samu wajen hadin kai a fannin tattalin arziki da na ciniki ya yi kyau, kuma mu'amala da daidaituwa da ake yi a kan batutuwan shiyya-shiyya da na kasa da kasa sun kara zurfafa, dangantakar tsakanin Sin da Australia tana cikin hali mai kyau a tarihi.

Mr. Hawker ya nuna cewa, kasar Sin za ta zama abokin ciniki mafi girma ta Australia, kuma yana fatan huldar tsakanin kasashen biyu za ta ci gaba da bunkasa bisa sakamakon da aka samu. Ya jaddada cewa, bangaren Australia yana bin manufar Sin daya tak, kuma ba za ta canza wannan manufa ba.

Mr. Alan Ferguson ya nuna cewa, cikin 'yan shekarun da suka wuce, majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta yi ta yin mu'amala da majalisar dokokin Australia, wannan ya ciyar da huldar tsakanin kasashen biyu gaba, yana fatan hukumomin kafa dokoki na kasashen biyu za su ci gaba da taka muhimiyyar rawa don sa kaimi ga kasashen biyu da su yi aikin hadin gwiwa mai kawo moriyar juna.(Asabe)