A ran 4 ga wata, shugaban kasar Sin Mr. Hu jintao wanda ke yin ziyarar aiki a kasar Australiya, ya gana da gwamna janar na kasar Australiya Mr. Michael Jeffery a birnin Canberra. Kuma Mr. Hu jintao ya bayyana cewa, "Mum yi imani cewa, dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Australiya za ta samu makoma mai haske. "
A gun ganarwa, Mr. Hu jintao ya nuna cewa, dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Australiya ta samu ci gaba mai kyau a cikin shekarun nan da suka wuce, kuma tana nan tana zama abar misali ga kasashen da suke da tsarin mulki dabban wajen yin mu'amalar aminci da hadin kan moriyar juna. Kuma ya kara cewa, ci gaba da zurfafa dangantakar kawance tsakanin Sin da Australiya yana dacewa da moriyar makoma ga duk bangarorin nan 2.
Mr. Michael Jeffery ya maraba da Mr. Hu jintao da hannu biyu biyu da ya yi ziyara a Australiya yayin da aka cika shekaru 35 da kafa dangantakar diplomasiyya tsakanin Sin da Australiya. Ya bayyana cewa, shugabannin kasashen nan biyu sun kaiwa juna ziyara sau da yawa, wannan ya sai kaimi ga bunkasuwar dangantakar bangarorin biyu. Cinikaya da ke tsakanin kasashen biyu tana bunkasa cikin gaggawa. Kuma kasashen biyu su yi mu'amala kan batutuwan kasa da kasa. (Zubairu)
|