Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-05 14:39:45    
Wace illa ce hauhawar farashin man fetur ya haifar ga kasashen Afirka?

cri

Manazarta sun bayyana cewa, hauhawar farashin zinariya da na tagulla da sauran kayayyakin da aka gyara bisa mataki na farko, da karuwar yawan kudadden waje da aka ajiye, da kuma raguwar nauyin bashin da aka ci, duk wadannan sun kara karfin kasashe masu shigo da man fetur na Afirka don magance hauhawar farashin mai. Ko da yake wasu kasashen Afirka ba su haka man fetur ba, amma suna fitar da zinariya da tagulla da sauran ma'adinai, wannan ya ba su taimako wajen biyan makudan kudin da suka kashe domin sayen man fetur daga kasashen waje.

Kan kasashe masu arzikin man fetur na Afirka kuwa, hauhawar farashin man fetur tana ta samar musu da dallar Amurka har ba fashi. Yawan kudin shiga da kasahen Nijeriya da Angola da Equatorial Guinea da sauran kasashe masu arzikin man fetur suka samu daga wajen man fetur da suka fitar zuwa kasashen waje ya karu-karuwar gaske. Kasar Angola kuma ta daidaita farashin kayayyaki na kasuwanni da kyau ta hanyar ba da kudi taimakon da ta samu daga wajen cinikin man fetur.

Amma, kada a kasa kula da hadarin da ta haifar ga kasashen Afirka sakamakon hauhawar farashin man fetur. Ban da wannan kuma hauhawar farashin man fetur ba ta inganta zaman jin dadi ga fararen hula na kasashe masu arzikin man fetur na Afirka ba, a akasin haka kuma ta zama wanin abun haifar da tashin kwanciyar hankali ga wadannan kasashe.(Umaru)


1 2