Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-05 09:26:15    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (29/08-04/09)

cri
Ran 2 ga wata,an kammala karo na 11 na gasar cin kofin duniya ta wasannin tsalle-tsalle da guje-guje a birnin Osaka na kasar Japan,kungiyar `yan wasan kasar Amurka ta samu lambobin zinariya 14 da na azurfa 4 da kuma na tagulla 8 ta zama zakara a kan jerin sunayen kungiyoyin da suka shiga takarar.A gun wannan gasar cin kofin duniya,ba a kago sabon matsayin koli na duniya ko daya ba.`Yan wasan tsalle-tsalle da guje-guje na kasar Sin su 57 ne suka shiga gasanni 25 domin neman samun lambar yabo,a gun gasannin da aka shafe kwanaki 9 ana yinsu,gaba daya `yan wasan kasar Sin sun samu lambar zinariya 1 da ta azurfa 1 da kuma ta tagulla 1.A gun gasar gudun tsallake shinge na mita 110 na maza,`dan wasa daga kasar Sin Liu Xiang wanda ke rike da matsayin koli na duniya ya samu zama na farko da dakika 12 da 95,wannan shi ne lambar zinariya ta farko da `yan wasa maza na kasar Sin suka samu a tarihinsu na shiga gasar cin kofin duniya. Ran 2 ga wata,an kawo karshen gasar ba da babbar kyauta ta wasan kwallon tebur ta kasar Sin ta gasar yawon kasa kasa ta wasan kwallon tebur ta duniya ta shekarar 2007,kungiyar `yan wasan kasar Sin ta samu dukkan lambobin zinariya 4.`Dan wasa Wang Hao ya samu zama na farko a gasar maza,`yar wasa Zhang Yinin ta samu zama ta farko a gasar mata,ban da wannan kuma Wang Hao da Ma Lin sun zama zakaran gasar dake tsakanin maza biyu biyu,Guo Yue da Guo Yan sun zama zakarar gasar dake tsakanin mata biyu biyu.

Ran 2 ga wata,an kammala gasa ta zango na farko ta gasanni a jere na duniyar wasan tsinduma cikin ruwa da kungiyar wasan iyo ta duniya ta shirya a birnin Sheffield na kasar Ingila.Kungiyar `yan wasan tsinduma cikin ruwa ta kasar Sin ta samu dukkan lambobon zinariya 8,wannan ya sake nuna wa kasashen duniya karfin kungiyar kasar Sin wadda ake kiranta da suna `kungiyar mafarki`.Za a yi gasa ta zango na biyu a ran 8 zuwa ran 9 ga wannan wata a birnin Mexico.

Ran 29 ga watan jiya,a hukunce ne `dan wasan kwallon kwando daga kasar Sin Yi Jianlian ya daddale yarjejeniya da kungiyar Milwaukee Bucks ta NBA ta kasar Amurka,daga nan Yi Jianlian ya zama `dan wasan kwallon kwando na hudu wanda ya shiga kungiyar NBA ta kasar Amurka a bayan Wang Zhizhi da Bater da kuma Yao Ming.

Kwanakin baya ba da dadewa ba,wakilin babbar hukumar kula da wasannin motsa jiki ta kasar Sin ya bayyana cewa,cibiyar yaki da magani mai sa kuzari ta kasar Sin za ta fara aiki kafin karshen wannan wata,ko shakka babu wannan zai kara karfafa aikin yaki da magani mai sa kuzari na kasar Sin.