Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-04 18:34:00    
Hu Jintao ya isa birnin Canberra domin ci gaba da yin ziyara a kasar Australia

cri

A ran 4 ga wata da yamma, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya isa birnin Canberra domin ci gaba da yin ziyarar aiki a kasar Australia.

Gwamnan kasar Mr. Michael Jeffery ya shirya gaggarumin biki a filin jirgin sama domin yin marhabin zuwan shugaba Hu. An harba bindiga har sau 21 don girmama, kuma 'yan bajudala sun buga taken kasashen Sin da Australia, daga baya kuma shugaba Hu ya duba faretin girmamawa da 'yan bajudala daga rundunar sojojin kasar Austsalia.

A birnin Canberra, shugaba Hu zai gana da gwamnan Australia da shugabannnin majalisun dattijai da wakilai na kasar. Kuma zai je wani filin makiyaya domin yin ziyara a gidajen makiyaya.

Shugaba Hu ya je birnin Canberra ne bayan da ya gama ziyararsa a birnin Perth. (Kande Gao)