Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-04 17:12:30    
Kasar Sin tana inganta ayyukan horar da likitoci na kananan hukumomi domin shawo kan cutar sukari

cri

Likitocin kananan hukumomin da suka shiga wannan kwas din horaswa bisa matsayinsu na dalibai sun mayar da martani sosai kan harkar, kuma suna ganin cewa, irin wannan harkar ba da ilmin shawo kan cututtuka tana da muhimmanci sosai ga matsakaita da kananan birane da kuma yankunan karkara, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da shirin ya daga matsayin likitocin wuraren wajen aiki da kuma kyautata fasahohin jiyya. Likita Hu Zhengqiang na asibitin jama'a na gundumar Linxia ta lardin Gansu da ke yammacin kasar Sin ya bayyana cewa, "Ta hanyar shiga wannan kwas din horaswa, mun kara fahimtar cutar sukari, kuma mun samu sabbin ilmi da dabaru wajen warkar da cutar, sabo da haka muka samu sakamako mai kyau. Ana ganin cewa, kungiyar shirya kwas din horaswa ta ba mu wata kungiyar jiyya da za ta kasance har kullum a cikin zukatanmu."

Bisa kididdigar da aka yi, an ce, ya zuwa watan Yuni na shekarar da muke ciki, wato karshen harkar "sabuwar babbar ganuwa wajen kiwon lafiya", likitoci fiye da dubu 32 na kananan hukumomi fiye da 1200 sun sa hannu a cikin harkar, ciki har da likitoci fiye da dubu 18 na gundumomin kasar Sin, da kuma dubu 14 na kauyukan kasar.

Furofesa Xu Zhangrong, kwararren farko na kungiyar kwararru masu ba da jagoranci da ke cikin harkar ya bayyana cewa, "shirin 'sabuwar babbar ganuwa wajen kiwon lafiya' wani mihimmin shiri ne. Tsawon hanyoyin da muka bi ya zarce kilomita dubu 100, kuma yawan likitocin kananan hukumomi da muka horar da su ya zarce dubu 30. Kafin wannan wadannan likitoci ba su da damar shiga irin wannan kwas din horaswa."

To, jama'a masu sauraro, shirinmu na yau na kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin ke nan. Muna fatan kun ji dadinsu, da haka a madadin Kande wadda ke fassara bayanin, Lawal nake cewa mako gobe war haka idan Allah ya kai mu.(Kande Gao)


1 2