
A ran 3 ga wata, a wata ziyara ba-zata da shugaban kasar Amurka Mr.Bush ya kai sansanin rundunar sojan jiragen sama na sojan Amurka da ke a lardin Anbar na kasar Iraq, wannan ziyara na karo 3 ne da shugaban Bush ya yi bayan da aka yi yakin Iraq.

Ran nan, Mr.Bush ya bayar da labari ga manema labaru, inda ya ce, ya sami labarin da babban kwamandan sojojin Amurka da ke kasar Iraq Mr.David Petraeus da jakadan kasar Amurka da ke kasar Iraq Mr.Ryan Crocker suka bayar, kuma a ganin Mr.Bush halin kwanciyar hankali na lardin Anbar na kasar Iraq ya yi kyau. Idan halin kwanciyar hankali na duk Iraq ya zama haka, mai yiyuwa yawan sojojin da suka mutu a kasar Iraq zai ragu. Amma Mr.Bush bai bayyana lokacin da sojojin Amurka za su janye ba.
Mr.Bush ya yi ziyarar ta ba-zata a kasar Iraq kafin ya halarta kwarya-kwaryar taron shugabannin na kungiyar APEC na karo 15. A lokacin da ya kai ziyarar kasar Iraq, ya yi shawarwarin tare da firyin ministan kasar Iraq Mr.Nuri Al-Maliki da shugabanni gwamnatin kasar Iraq da shugabannin kabilun lardin Anbar, kuma zai sami labarin da manyan jami'an kasar Amurka da ke a kasar Iraq suka bayar.(Abubakar)
|