Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-04 13:58:51    
(Sabunta) Hu Jintao ya isa birnin Perth domin soma ziyarar aiki a Australiya

cri

Bisa gayyatar da gwamna janar na kasar Australiya Michael Jeffery da firaministan kasar John Howard suka yi masa ne, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya isa hedkwatar jihar yammacin Australiya wato Perth jiya 3 ga wata da dare, domin fara yin ziyarar aiki a kasar Australiya, kuma zai halarci kwarya-kwaryar taron shugabannin kunigyar hadin kan tattalin arzikin yankunan dake bakin tekun Pacific, wato APEC da za a yi a birnin Sydney.

Shekarar da muke ciki shekara ce ta cika shekaru 35 da kafuwar huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Australiya, wannan ne kuma karo na biyu da shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya sake kai wa kasar Australiya ziyarar aiki bayan shekaru hudu da suka gabata. A cikin jawabinsa a rubuce da ya bayar a filin saukar jirgin sama bayan da ya isa birnin Perth, shugaba Hu ya fadi cewa, makasudin ziyararsa ta wannan gami shi ne domin kara nuna amincewa da juna, da kara samun ra'ayi daya da kuma zurfafa hadin gwiwa da yunkurin neman kyakkyawar makoma tsakanin kasashen biyu. A cikin jawabinsa ya kara da cewa, kasashen Sin da Australiya dukkansu muhimman kasashe ne dake yankin bakin tekun Pacific, bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da Australiya na dacewa da babbar moriyar kasashen biyu da jama'arsu, haka kuma tana sa kaimi ga wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da neman samun fa'ida a shiyyar da suke ciki har ma a duk fadin duniya.

Ran nan da dare, shugaba Hu Jintao ya yi wata ganawa da gwamnan jihar yammacin Australiya Alan Cappenter, inda ya furta cewa, kasar Sin tana dora muhimmaci kan raya huldar abokantaka dake tsakaninta da Australiya, kuma za a samu kyakkyawar makoma wajen hadin gwiwarsu. A cikin 'yan shekarun nan, kasar Sin ta rigaya ta kasance kasaitacciyar kasuwa ta farko wajen shigar da kayayyakin jihar yammacin Austrliya kuma aminiya ta biyu mafi girma wajen yin cinikayya tare da jihar. Shugaba Hu ya bayyana cewar, kasarsa na fatan yin kokari tare da jihar yammacin Australiya domin kai hadin gwiwarsu zuwa wani sabon matsayi.(Murtala)