Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-03 21:41:58    
Wasu labaru game da kabilun kasar Sin

cri

---- Kwanan bayan an rufe bikin Shoton na shekarar 2007 da aka shirya a birnin Lhasa na jihar Tibet ta kasar Sin, a gun bikin an shirya bukukuwa masu ban sha'awa iri daban-daban.

Bikin Shoton bikin gargajiya ne na 'yan kabilar Tibet, an fara yi wannan biki ne tun daga karni na 11. Kamar yadda aka yi a shekarun baya, zane-zanen addinin Buddha da aka nuna a wurin ibada na Zhabung sun zama daya daga cikin muhimman bukukuwan da aka yi a gun bikin Shoton, inda ya jawo hankulan duban jama'a masu bin addinai wadanda suka je ziyara da yin sujada a gaban wani babban zanen Thangka na Sakyamuni. Bisa kididdigar da kwamitin shirin bikin Shoton na birnin Lhasa ya yi an ce, yawan jama'a masu bin addinai da masu yawon shakatawa da suka kalli zane-zaben addinin Buddha a wajen bikin da ake yi a wannan shekara a wurin ibada na Zhaibung ya kai fiye da dubu 180.

An shirya bukukuwan nuna wasannin fasaha fiye da 20 a gun bikin Shoton na wannan shekara. Ban da wannan kuma an yi bukukuwan al'adu da yawon shakatawa da yin harkokin kasuwanci.

---- Yanzu lokaci ya yi domin yin yawon shakatawa a jihar Tibet, masu yawon shakatawa da yawa suna son kwana cikin hotel irin na gidajen 'yan kabilar Tibet ta yadda za su iya more dabi'un 'yan kabilar.

A kan shahararen titin Barkor na birnin Lhasa, da akwai farfajiya da yawa wadanda aka yi musu gyare-gyare don su zama hotel-hotel. An ce, irin wadannan hotel ba su da tsada, wato daki daya dake dauke da mutane 2 yakan dauki kudin Reminbi na kasar Sin Yuan 80 kawai a kowace rana. Kuma akan ci abinci irin na kabilar Tibet, a dare kuma akan yi wake-wake da raye-raye na kabilar Tibet cikin farfajiyar. Wani mai yin hidima na hotel ya bayyana cewa, tun farkon lokacin zafi na wannan shekara zuwa yanzu, yawan ire-iren wadannan hotel da suka karbi masu yawon shakatawa ya wuce kashi 80 bisa 100, daga cikin masu yawon shakatawa da suka karba, yawancin su kuma masu zaman kansu ne.

Bisa kididdigar da hukumar kula da yawon shakatawa ta Tibet ta yi an ce, yanzu da akwai hotel da yawa daga cikin hotel-hotel masu taurari da ake da su a jihar Tibet su zama irin na gidaje na kabilar Tibet. Wasu manoma da makiyayya su ma sun yi kokarin bude hotel-hotel irin na gidaje domin jawo hankulan masu yawon shakatawa da su yi kwana a ciki, kuma da haka ne za su iya samun kudin shiga da yawa. (Umaru)