
Bisa gayyatar da babban gwamnan kasar Australiya Michael Jeffery da firayin ministan kasar John Howard suka yi masa, a ran 3 ga wata da safe, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya tashi daga birnin Beijing, domin kai ziyarar aiki a kasar Australiya, da kuma halartar kwarya kwaryar taro na karo na 15 na shugabannin kasashen kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki ta kasashen Asiya da tekun Pacific wato APEC.
Bana shekara ce ta cikon shekaru 35 da kafuwar dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Australiya. A lokacin, Hu Jintao zai sake kai wa kasar Australiya ziyarar aiki bayan shekaru hudu da suka wuce, wato bayan ziyararsa a kasar a karo da ya gabata. Babban taken taron koli na kungiyar APEC na bana shi ne, 'a kara inganta iyalan kungiyar APEC, domin samun wata kyakkyawar makoma mai dorewa tare'. A gun taron koli kuma, Hu Jintao zai gabatar da ra'ayoyin kasar Sin dangane da sauyawar yanayi, da bunkasuwar kungiyar APEC da dai sauransu.(Danaldi)
|