Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-31 15:32:39    
Shahararren gwanin fasaha daga kasar Amurka zai rubuta waka ta babban take domin taron wasannin Olympics na Beijing

cri

Tare da kusantowar shekarar 2008, taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing a shekarar 2008 sai kara jawo hankulan jama'ar kasar Sin da kuma na duk duniya yake a kowace rana. A matsayin wani gagarumin taron wasannin motsa jiki na duk duniya, ba ma kawai gwamnatin kasar Sin da jama'arta sun mai da hankali sosai kan taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing a shekarar 2008 ba, har ma mutane daga da'irori daban daban na duk duniya sun zura ido sosai a kai, ciki har da shahararren mutum mai suna Quincy Jones daga da'irar kade-kade da wake-wake ta kasar Amurka.

A shekarar 1985 ne aka rubuta wannan waka kuma shahararren mawaki mai suna Michael Jackson da kuma sauran mashahuran mawaka fiye da 10 na duniya suka rera wakar domin bada agaji ga jama'ar Nahiyar Afrika dake fama da yunwa. Mr. Quincy Jones shi ne ya rubuta wannan waka. Abu mai ban sha'awa shi ne Mr. Quincy Jones ya taba tsara shirin watsa waka ta farko mai dadin ji a kan wata. Kuma shi wani gwanin fasaha ne, wanda ya taba samun lambar yabo mai daraja ta Oscar da ta Grammy ; kuma shi mai jin kai da dan gwagwarmaya ne na kasar Amur'ka wanda ya fi shahara a duniya wajen kiyaye hakkin bil adama.

Kwanakin baya ba da dadewa ba, Mr. Quincy Jones mai shekaru 73 da haihuwa ya zo nan babban yankin kasar Sin a karo na farko cikin zaman rayuwarsa. A duk tsawon lokacin da yake zama a nan kasar Sin, ya ziyarci ni'imtattun wurare da tsoffin wuraren tarihi ,da jami'o'I da kolejoji da kuma tituna na birnin Beijing da na Shanghai wato shahararrun birane guda biyu na kasar Sin domin duba kyakkyawar sura. Muhimmin makasudin zuwan Mr. Jones da kuma kungiyarsa nan kasar Sin ba wai yin yawon shakatawa kawai ba, ya zo nan ne musamman domin bayyana kyakkyawan burinsa na rubuta waka ta babban take domin taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing a shekarar 2008. A matsayin wani shahararren mai kirkiro kade-kade da wake-wake, lallai Mr. Jones ya gwanance a fannin ilmin al'adu da fasaha. Ya hakkake, cewa tare da kara bude kofa ga kasashen waje da gwamnatin kasar Sin take yi a fannin al'adu da fasaha, labuddah zai iya kara shigo da kade-kade da wake-wake cikin kasuwannin kasar Sin. A ganinsa, wannan dai musanye-musanye ne ake yi tsakanin kasashen Sin da Amurka a fannin al'adu, haka kuma wani abu ne da zai kawo masa riba mai tsoka. Ban da wannan kuma Mr. Jones ya yi matukar farin ciki da fadin cewa lallai wata kyakkyawar dama ce gare shi saboda ya shiga cikin yunkurin share fage ga shirya taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijinga shekarar 2008. ya furta, cewa: 'Ina alfahari matuka da samun damar rubuta wata waka ta babban take ta taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing a shekarar 2008. Na fadi abun da ya fito daga zuciyata, cewa ban yi tsammanin samun damar watsa wa duk duniya labarin cewa wace irin kasa ce kasar Sin ba'.

Mr. Jiang Xiaoyu, mataimakin shugaban kwamitin shirya taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing ya fada wa wakilinmu, cewa kwamitin ya yi farin ciki matuka da ganin shiga cikin aikin rubuta waka ta babban take ta taron wasannin Olympics na Beijing da sannannen mawallafin wakoki wato Mr. Jones dake kan matsayin muhimmanci kamar haka ya yi. Ko shakka babu shigar Mr. Jones cikin wannan muhimmin aiki mai girma za ta sa kaimi ga gwanayen fasaha na gida da na waje don su sa hannu cikin taron wasannin Olympics na Beijing. Mr. Jiang Xiaoyu ya furta, cewa 'Mr. Jones wani shahararren kwararre ne a duniya a fannin kade-kade da wake-wake. Muna girmama shi kwarai da gaske, kuma mun sa ran alherin cewa waka ta babban take da Mr. Jones zai bai wa taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijig za ta shere mutane kwarai da gaske'.

Bugu da kari kuma, ya bayyana, cewa kafin a kira taron wasannin Olympics na Beijing, kwamitin shirya taron wasannin zai gudanar da babbar gasar karbar wakoki na wasannin Olympics a kowace shekara. Kuma za a tabbatar da waka ta babban take ta taron wasannin Olympics ne a shekarar 2008.

Ko da yake Mr. Jones bai dade yana morewa a nan kasar Sin ba, amma dukkan abubuwan da ya gani ko ya ji sun burge shi kwarai da gaske.( Sani Wang )