Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-31 12:17:46    
Kasashen Afirka sun hada kansu domin yin adawa da kasar Amurka wajen kafa hedkwatar sojanta a Afirka

cri

A ran 29 ga watan Agusta na shekarar da muke ciki, ministan tsaron kasar Afirka ta Kudu Mosiuoa Lekota ya yi bayani a gun wani taron majalisar dokoki ta kasar da aka yi a birnin Cape Town, babban birnin kasar, cewa Afirka ba ta yin marhabin da kasancewar sojojin kasashen waje a nahiyar, musamman ma ta nuna adawa da kasar Amurka wajen kafa sansanin soja a Afirka ta hanyar kafa hedkwatar soja. A waje daya kuma ya sanar da cewa, kungiyar bunkasa kudancin Afirka wato SADC da take kunshe da kasashen Afirka ta Kudu da Namibia da Zambia da dai sauran kasashe 11 ta riga ta tsai da kudurin cewa, ko wace kasa membar kungiyar ba za ta karbi sojojin Amurka ba. Sabo da haka Amurka ta sake jin takaici wajen zabar wurin kafa hedkwatar sojanta bayan da ta samu rashin amincewa a arewacin Afirka.

A ran 6 ga watan Fabrairu na shekarar da muke ciki, kasar Amurka ta sanar da kafa hedkwatar sojanta a Afirka domin daidaita da kuma sa ido kan harkokin sojan Amurka da aka yi a nahiyar Afirka ban da kasar Masar. Kuma tana cikin shirin kaddamar da aikin daga ran 30 ga watan Satumba na shekara mai zuwa. Haka kuma ma'aikatar tsaron kasar Amurka tana ganin cewa, aikin da hedkwatar sojan Amurka da ke Afirka za ta tafiyar shi ne tallafa wa Afirka wajen samun kwanciyar hankali da tsaron kai ta hanyar hadin gwiwa tare da kasashe daban daban na Afirka da kuma kungiyoyin Afirka. A watanni da dama da suka gabata, har kullum tawagar ma'aikatar tsaron kasar Amurka tana yin ziyara a kasashen Afirka domin lallashinsu wajen karbar shirin. Amma irin wannan kyakkyawan hali na wai da kasar Amurka ta nuna daga wajenta ne kawai.

A watan Maris na shekarar nan, kasar Algeria ta bayyana a fili cewa, ba ta amince da kasar Amurka ta kafa hedkwatar soja a yankinta ba, haka kuma ba ta yarda da ko wace kasa wajen kafa sansanin soja a kasar ba. Daga baya kuma kasashen Morocco da kuma Libya sun nuna rashin amincewa da Amurka a kan batun. Bugu da kari kuma kasashen Algeria da Libya sun bayyana cewa, sun ki amincewa da kasar Amurka da ta kafa hedkwatar sojanta a ko wace kasar da ke makwabtaka da su.

Yanzu adawa da kungiyar SADC ta nuna wa Amurka wajen kafa hedkwatar soja a Afirka ya shaida cewa, kasashen Afirka sun riga sun samu ra'ayi daya kan batun kafa hedkwatar sojan Amurka a Afirka. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da sun san ainihin nufin Amurka a kan batun, wato Amurka tana son karfafa kasancewar sojanta a Afirka da kuma sa baki a cikin manyan albarkatun nahiyar Afirka.

Bisa sabuwar kididdagar da gwamnatin kasar Amurka ta bayar, an ce, yawan danyen man fetur da Amurka ta shiga daga Afirka a shekara ta 2006 ya kai garewani miliyan 2.23 a ko wace rana, sabo da haka Afirka ta zama wuri mafi girma ga Amurka wajen shiga da danyen man fetur. Kwararrun Amurka sun kiyasta cewa, ya zuwa shekara ta 2010, watakila yawan man fetur da Afirka za ta fitar zai zarce kashi 20 cikin dari na duk duniya, kuma kashi 25 cikin dari na men fetur da Amurka za ta bukata a shekaru 10 masu zuwa zai zo daga shiyyar Afirka da ke saharar hamada ta kudu.

Kafin kafuwar hedkwatar sojan Amurka a Afirka, sojan Amurka ya riga ya kara tsoma baki cikin harkokin soja na Afirka ta hanyar shirya atisayen hadin kai da dai sauransu. A farkon rabi na shekara ta 2006, kungiyar tasro ta NATO da ke karkarshin jagorancin Amurka ta taba yin gaggarumin atisaye a cikin yankin kasar Cape Verde, wata kasa tsibiri ce da ke yammacin Afirka, kuma wannan shi ne karo na farko da sojojin kungiyar tsaro ta NATO suka yi harkokin soja a Afirka. Ban da wannan kuma, sojan Amurka ya riga ya kafa wani sansanin din din din a kasar Djibouti da ke gabashin Afirka, da kuma jibge wata rundunar sojojin da yawanta ta kai kusan 1700 domin sarrafa mashigin tekun red sea da kuma tafiyar da ayyukan tattara labaran yaki da ta'addanci.

Har kullum kasashen Afirka suna tsayawa tsayin daka kan cewa, ya kamata a warware matsalolin Afirka ta kungiyar tarayyar Afirka da kuma 'yan Afirka su kansu a maimakon tsoma bakin da kasashen waje suka yi. Sabo da haka ko shakka babu za su nuna rashin amincewa a bayyane ga fadadar ayyukan sojan Amurka na wai domin yaki da ta'addanci a duk duniya, amma a hakika dai domin neman albarkatu. Kamar yadda ministan harkokin waje na kasar Algeria Mohammed Bedjaoui ya bayyana a watan Maris na shekarar nan, kafa hedkwatar sojan Amurka a Afirka bai dace da ka'idar da kasashen Afirka suke tsayawa tsayin daka a kai wajen samun 'yancin kai da kuma cikakken yankin kasa (Kande Gao)