Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-30 20:59:33    
Ministan harkokin waje da na kasuwanci na kasar Sin za su halarci taron ministoci a karo na 19 na kungiyar APEC

cri
Yau 30 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Mr. Liu Jianchao ya sanar da cewa, ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi, da ministan kasuwanci na kasar Bo Xilai, za su shugabanci kungiyar wakilai tare, don halartar taron ministoci a karo na 19 na kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki ta Asiya da Pacific, wato APEC da za a shirya a birnin Sydney na kasar Australia, za a kira taron ne domin shiryawa kwarya-kwaryar taron shugabanni a karo na 15 na APEC da za a shirya ba da dadewa ba.

A gun taron ministoci na wannan karo, za a mai da hankali kan tattauna batutuwan ba da taimako ga shawarwarin kungiyar WTO na zagaye na Doha, da neman hadin kai na shiyya-shiyya wajen tattalin arziki, da zuba jari a fannin ciniki, da hadin gwiwar fasaha wajen tattalin arziki, da tsaron dan Adam, da yaki da cin hanci da rashawa, da gyare-gyaren tsari, da kuma gyare-gyaren APEC, da dai sauransu. (Bilkisu)