Don biyan bukatun zaman al`umma da kuma kyautata ingancin sabbin sana`o`i,a cikin shekaru biyar da suka shige,ma`aikatar kwadago da ba da tabbaci ga zaman rayuwar jama`a ta kasar Sin tsara ma`aunin sabbin sana`o`i 52.A shekarar bara,ma`aikatar nan ta kafa tsarin sanar da sabbin sana`o`i.Ya zuwa yanzu,gaba daya ma`aikatar ta riga ta sanar da sabbin sana`o`i 19 ga zaman al`umma,wadannan sabbin sana`o`i sun hada da sha`anin IT da sha`anin ba da shawara da sauransu.Dalilin da ya sa haka shi ne domin gwamnatin kasar Sin ta mai da hankali kan sha`anin kera kayayyaki da sha`anin IT da sha`anin ba da hidima.A sa`i daya kuma,saboda ingancin zaman rayuwar jama`a ya sami kyautatuwa,shi ya sa wasu sana`o`i dake cikin sha`anin ba da hidima kamasu mai aikin jiyya ga lafiyar dabbobi da ake ajiye a gida da mai aikin kwalliya ga mota da sauransu sun fito.Ban da wannan kuma,bunkasuwar wasu sha`anonin kasar Sin ita ma ta kago muhalli mai kyau ga fitowar sabbin sana`o`i.Alal misali,a cikin `yan shekarun da suka shige,sha`anin taron nune-nune ya sami bunkasuwa cikin sauri a nan kasar Sin,wannan ya sa aikin ba da shawara kan shirya taron nune-nune ya zama wani sabon sana`a.Mun sami labari cewa,kawo yanzu,yawan masu ba da shawara kan shirya taron nune-nune a kasar Sin ya riga ya kai fiye da dubu daya.
Ban da wannan kuma,akwai sauran sabbin sana`o`i da yawa a kasar Sin,ma`aikatar kwadago da ba da tabbaci ga zaman rayuwar jama`a ta kasar Sin za ta ci gaba da sanar da su a nan gaba.(Jamila) 1 2
|