Kwanan nan, mun sami dimbin wasiku daga wajen masu sauraronmu, inda masu sauraronmu suka bayyana ra'ayoyinsu dangane da shirye-shiryenmu tare kuma da ba mu shawarwari. Mohammed Talle daga jihar Kano, tarayyar Nigeria ya rubuto mana cewa, ina so in baku wadansu shawarwari kamarka:
a. A samar da wani tsari wanda zai sa duk wani mai son koyon Sinanci, to ya zamana akwai wata jarrabawar da za a rinka yi masa ko dai a sati biyu-biyu, ko kuma a wata-wata domin tabbatar da ingancin abubuwan da ake koyawa jama'a.
b. Kuma a samar da takardun koyo ga duk wanda ya bukata wanda zai rinka cike amsoshinsa yana turowa, watau ta hanyar Wasika ko tahanyar Internet
c. A samar da SATIFIKET ga duk wanda yayi kwazo akan abubuwan da aka tambaye su.
To, Mohammed, mun gode maka da kyawawan shawarwarin da ka ba mu, gaskiya shawarwarinka suna da kyau kwarai, kuma sun tuno mu hanyoyin da za mu bi don kyautata shirinmu na koyon Sinanci, mun gode. Muna fatan da Mohammed Talle da sauran masu sauraronmu za ku rinka ba mu irin kyawawan shawarwarinku, ta yadda za mu kyautata shirye-shiryenmu cikin hadin gwiwa.
Sai kuma malam Bala Danazumi da ya fito daga birnin Zaria da ke jihar Kaduna, tarayyar Nijeriya, ya turo mana wasikarsa, inda ya ba mu wasu shawarwari kan shirye-shiryenmu, to, ga yadda shawarwarinsa suka kasance. Ya ce, ra'ayina dangane da shirye-shiryenku, shi ne ya kamata a kara wa wadansu shirye-shiryen lokaci, ko da minti talatin ne, kamar su filin koyon sinanci wanda kuke gabatarwa a ko wace rana da kananan kabilu da Yawon shakatawa da dai sauransu. Sai kuma shirin nan na Bayanin Musamman na mu leka kasar Sin dukansu suna da mahimmaci.
To, muna godiya ga Bala Danazumi da ya ba mu wadannan shawarwari, wadanda suka nuna kaunarsa da kulawarsa ga shirye-shiryenmu, mun gode, kuma a game da shawarwarin, za mu yi nazari sosai a kansu, kuma nan gaba kadan, muna so mu gabatar da gyare-gyare a kan shirye-shiryenmu, ga shi kuma shawarwarin sun nuna mana hanya ke nan, to, mun gode.
Bayan haka, mun kuma sami wasika daga wajen Rabe Mamane, mazaunin birnin Yamai, jamhuriyar Nijer, kuma wasikarsa ta ba mu kwarin gwiwa kwarai. Ya ce, Ni dai tsohon mai saurarenku ne, fiye da shekaru goma, amma sai yau Allah ya sa na samu damar rubuto muku da wasikata. Muna jin dadin sauraren shirye-shiryenku a bisa tashar Radio R&M a nan birnin Yamai. To, mun gode, Rabe mamane, gaskiya mun yi farin ciki da ganin masu sauraronmu da ke birnin Yamai suna jin dadin shirye-shiryenmu da muka watsa ta tashar rediyon R?M, mun gode, kuma muna fatan masu sauraronmu da ke birnin Yamai za ku ci gaba da ba mu goyon baya, ku rinka rubuto mana, ku fada mana ra'ayoyinku da shawarwarinku kan shirye-shiryenmu. Allah ya bar zumunci a tsakaninmu.
Sai kuma Yusuf Abdullahi daga Yola jihar Adamawa ya aiko mana Email cewa, da farko ina mai farin cikin samun dama na turo muku wasika a wannan lokaci bayan tsawon lokaci ba ku ji na, hakan ya faru ne saboda makaranta da na ke yi, to amma yanzu na kammala karatuna. Ni ne tsohon mai sauraronku yusuf Abdullahi daga jihar Adamawa a tarayyar Nigeriya, amma yanzu Allah ya ba ni ikon mallakar email wadda ina fatan cikin sauki za mu karfafa zumuncin dake tsakaninmu fiye da a baya. A karshe ina mai jinjina muku wajen ilmantar da mu (masu sauraronku) da shirye shirye masu kayatarwa. To, madallah, Yusuf, adireshin Email dinka mun riga mun samu, kuma muna farin ciki, sabo da ta hanyar Email ne muka fi samun saukin tuntubar juna, wadda muke fatan za ta iya taimakawa wajen karfafa dankon zumunci a tsakaninmu. Bayan haka, da malam Yusuf da dai sauran masu sauraronmu, kada ku manta da adireshinmu na internet, wato hausa@cri.com.cn, da fatan za ku dinga rubuto mana bisa wannan adireshinmu na Email.
Dukan masu sauraron sashen Hausa na rediyon kasar Sin, idan kuna da shawarwari ko kuma ra'ayoyi a dangane da shirye-shiryenmu, muna kuma fatan za ku dinga turo mana, domin da su ne za mu kara samun ci gaba a kullum. Da fatan Allah ya bar zumunci a tsakaninmu. Kada kuma ku manta kuna iya kama mu a akwatin gidan wayarmu a kasar Nijeriya, wato Lagos Bureau, China Radio International P.O.Box 72100, Victoria Island, Lagos Nijeriya. ko kuma ku aiko mana wasiku zuwa nan kasar Sin, wato, Hausa Service CRI-24, China Radio International, P.O.Box 4216, Beijing, P.R.China,100040. kuna kuma iya aiko mana Email a kan Hausa @cri.com.cn.(Lubabatu)
|