![]( /mmsource/images/2007/09/03/m07090301.jpg) Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya bayyana a yau 29 ga wata a nan birnin Beijing cewa, Sin tana nuna goyon bayanta ga tattauna batun tinkarar sauye-sauyen yanayi a gun kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC, kuma tana fatan za a cimma nasarori a kan batun.
A yayin da yake hira da John Howard, firaministan kasar Australia ta wayar tarho, shugaba Hu Jintao ya yi nuni da cewa, sauye-sauyen yanayi yana shafar dauwamammen cigaban duniya, yana kuma shafar zaman alheri na dan Adam. Gwamnatin kasar Sin tana dora muhimmanci sosai a kan batun sauye-sauyen yanayi, tana fatan a gun kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC da za a yi ba da dadewa ba, bangarori daban daban za su yi shawarwari, kuma su sami nasarorin da za su iya bayyana ra'ayi daya na bangarori daban daban.(Lubabatu)
|