Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-29 18:17:13    
Kasar Sin ta kafa doka domin raya tattalin arzikin bola jari

cri
A makon da muke ciki yanzu, zaunannen kwamitin majalisar dokokin kasar Sin yana taro a nan birnin Beijing. Wasu daftarin dokokin da suke da nasaba da kokarin yin tsimin makamashi da kiyaye muhalli sun jawo hankulan mutane na gida da na waje sosai. Daga cikinsu, daftarin dokar tattalin arzikin bola jari da aka gabatar da shi a karo na farko domin dudduba shi ya fi jawo hankulan mutane. An bayyana cewa, bayan kaddamar da wannan dokar tattalin arzikin bola jari, za ta bayar da gudummowa wajen yin amfani da makamashi da kiyaye da kyautata muhalli, kuma za ta taka muhimmiyar rawa wajen kokarin neman bunkasuwa cikin hali mai dorewa.

Lokcin da yake tabo magana kan amfanin dokar tattalin arzikin bola jari da dalilin da ya sa ake gaggauta kafa wannan doka, Mr. Fan Zhijun, mataimakin shugaban kwamitin kiyaye muhalli da albarkatun halittu na majalisar dokokin kasar Sin, ya ce, "Dalilan da suka sa raya tattalin arzikin bola jari su ne, da farko dai neman sabon makamashi domin raya tattalin arziki, sannan za a iya rage abubuwa masu gurbata muhalli da ake fitarwa. Bugu da kari kuma, za a iya kara samun moriya daga wajen tattalin arziki. Za a iya raya tattain arzikin bola jari ne a karkashin ka'idojin doka daya, kuma za a tabbatar da samun albarkatun halittu da muhalli mai kyau wajen raya tattalin arziki, kuma za a iya tabbatar da cewa, bunkasuwar tattalin arziki za ta bayar da gudummowa wajen sa kaimi kan kokarin yin tsimin makamashi da kyautata muhalli. Sabo da haka, abu ne da ya wajaba a gaggauta kafa dokar tattalin arzikin bola jari."

A karshen karni na 20 da ya gabata ne an soma kafa dokokin sa kaimi wajen raya tattalin arzikin bola jari a duk fadin duniya, musamman a kasashen Jamus da Japan da kasashen kungiyar Tarayyar Turai. Ya kasance da bambanci a tsakanin dokar tattalin arzikin bola jari ta kasar Sin da ta sauran kasashen duniya. Mr. Fan Zhijun ya ce, "A kasashen yammacin duniya, an fi mai da hankali wajen sake yin amfani da shara. Amma yanzu kasar Sin tana cikin lokacin neman bunkasuwar masana'antu cikin sauri. Ana amfani da kuma bata albarkatun halittu sosai, ana kuma gurbata muhalli kwarai. Sabo da haka, za a iya samun damar rage yawan makamashin halittu da masana'antu ke amfani da shi. Sabo da haka, za mu kara mai da hankali kan yadda za mu rage yawan makamashin halittu da ake amfani da shi a cikin masana'antu."

Sabo da haka, yaya za a sa ido kan masana'antu wadanda suke amfani da makamashin halittu da ruwa sosai yana daya daga cikin muhimman abubuwa a cikin daftarin dokar tattalin arzikin bola jari. A cikin wannan daftarin, gwamnatin kasar Sin za ta kara sa ido kan masana'antun narke karfe da na kwal da na samar da wutar lantarki da kamfanonin da suke da nasaba da man fetur da kayayyakin guba wadanda su kan yi amfani da ruwa fiye da shirin da aka tsara.

Bugu da kari kuma, kasar Sin za ta dauki matakan sa kaimi kan kokarin tsimin makamashin halittu da kiyaye muhalli bisa doka domin raya tattalin arzikin bola jari. Mr. Fan ya bayyana wa wakilinmu irin wadannan matakai, cewar "Za a kafa asusun musamman na raya tattalin arzikin bola jari, kuma za a samar da kudin tallafi ga muhimman shirye-shiryen kimiyya da fasaha da suke da nasaba da tattalin arzikin bola jari. Bugu da kari kuma, za a fitar da manufofi masu gatanci wajen buga haraji kan tattalin arzikin bola jari."

Bisa labarin da wakilinmu ya samu, an ce, tun daga shekarar 2005 ne aka soma tsara daftarin dokar tattalin arzikin bola jari a nan kasar Sin. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, gwamnatin kasar Sin ta riga ta soma gwajin aikin raya tattalin arzikin bola jari a wasu masana'antun narke karfe da na guba wadanda suke unguwannin raya tattalin arziki da unguwannin aikin gona na kasar ko a wasu lardunan kasar. (Sanusi Chen)