Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-29 15:26:05    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(23/08-29/08)

cri
A kwanan baya, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya gabatar da sakamakon aiki na mataki na farko na sayar da tikitin kallon taron wasannin Olympic na Beijing ga al'ummar kasar a gida. Mutanen Sin fiye da dubu 300 sun sami nasarar yin rajistar sayen tikitin shiga 1,533,345. Kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya kaddamar da sayar da tikitin shiga ga al'ummar kasar Sin a gida a mataki na farko a ran 15 ga watan Afril na wannan shekara.

Wata sabuwar kuma, a ran 21 ga wata, a nan Beijing, wani jami'in hukumar kiyaye muhalli ta Beijing ya sanar da cewa, jarrabawar ba da tabbaci ga gasannin motsa jiki na 'Good Luck Beijing' ta fuskar muhalli da zirga-zirga ta sami sakamako mai kyau, wadda aka yi tun daga ran 17 zuwa ran 20 ga wata a nan Beijing. A cikin wadannan kwanaki 4, ingancin iskar Beijing ya biya bukatar yin gasannin motsa jiki kwata-kwata. Jarrabawar ta bai wa Beijing bayanai masu dimbin yawa wajen tsara 'shirin kyautata muhalli a lokacin taron wasannin Olympic'.

Ran 25 ga wata, a birnin Osaka na kasar Japan, an bude gasar fid da gwani ta wasan tsalle-tsalle da guje-guje ta kasa da kasa a karo na 11. 'Yan wasa fiye da dubu 2 daga kasashe da yankuna 203 na duk duniya sun shiga gasar. Kasar Sin ta aika da 'yan wasanta 57 don shiga kananan gasanni 25, a ciki kuma har da malam Liu Xiang, wanda ya rike da matsayin bajimta na duniya na wasan gudun ketare shinge mai tsawon mita 110, shi ne kuma zakara a gun taron wasannin Olympic na Athens a shekarar 2004, ban da wannan kuma, an mayar da shi dan wasa ne da mai yiwuwa ne zai sami lambar zinariya a wanna karo. Za a rufe gasar fid da gwani ta wasan tsalle-tsalle da guje-guje ta duniya a wannan karo a ran 2 ga watan Satumba.

Ran 26 ga wata, a birnin Ningbo da ke gabashin kasar Sin, an kammala gasanni na karon karshe na gasar ba da babbar kyauta ta wasan kwallon raga ta duniya a tsakanin mata a shekarar 2007. A cikin gasa ta karshe da aka yi, kungiyar wasan kwallon raga ta mata ta kasar Sin ta lashe takwararta ta kasar Brazil da cin 3 da ba ko daya, ta haka ta zama ta biyu saboda samun nasara a cikin gasanni 4 daga cikin dukkan gasanni 5 a wannan karo. Kungiyar kasar Netherlands kuwa ta zama zakara domin samun nasara a cikin dukkan gasanni 5.(Tasallah)