|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2007-08-28 21:36:37
|
|
Hu Jintao zai bayyana ra'ayin kasar Sin da kuma matsayin da kasar ke tsayawa a kai dangane da yunkurin hadin gwiwa na Asiya da Pacific
cri
Ranar 28 ga wata a nan birnin Beijing, wani jami'in ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ya bayyana cewa, a gun kwarya-kwaryar taron shugabanni a karo na 15 na kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki ta Asiya da Pacific, wato APEC, wanda za a shirya a nan gaba ba da dadewa ba, shugaba Hu Jintao na kasar Sin zai bayyana ra'ayin kasar Sin da kuma matsayin da kasar ke tsayawa a kai kan yunkurin hadin gwiwa na Asiya da Pacific, da kuma batun magance sauyin yanayi.
Wannan jami'i ya bayyana cewa, kasar Sin na fata za a daddale da bayar da sanarwar Sydney game da sauyin yanayi a gun taron shugabanni, kuma za a zartas da rahoton neman hadin kan tattalin arziki na yankin Asiya da Pacific, bugu da kari kuma za a sa kaimi ga samun sakamako mai kyau tun da wuri wajen shawarwarin kungiyar WTO a zagaye na Doha, da kuma daukaka ci gaban yunkurin gyare-gyaren kungiyar APEC. Ya bayyana cewa, kasar Sin na son yin kokari tare da bangarori daban daban, domin tabbatar da wadannan makasudai. (Bilkisu)
|
|
|