A cikin birnin Wuhai da ke tsakiyar jihar Mongolia ta gida mai cin gashin kai ta kasar Sin, akwai wani kamfanin kula da harkokin sarrafa ma'adinin kwal da gawayi wanda ake kiransa Shenhua. A da, sarrafa ma'adinin kwal wata sana'a ce da ke iya gurbata muhallin halittu mafi tsanani, amma yanzu, lokacin da wakilinmu ya shiga filin samar da kayayyaki na wannan kamfani, ya yi ban mamaki sosai. A gaban idanunsa, ko ina yana da tsabta a maimakon warin da a kan taba shaka a masana'antun samar da kwal a lokacin da. Shugaban kamfanin Li Huaiguo ya gaya mana cewa, kamfaninsa yana dora muhimmanci sosai kan kiyaye muhallin halittu, yana ta yin nazari kan sabbin fasahohi wajen daidaita abubuwa masara amfani na kwal da gawayi da kuma sake yin amfani da su, kuma yanzu an riga an samu wata hanya wajen tsimin makamashi da kuma kiyaye muhalli. Kuma ya kara da cewa,
"A da, mu kan zubar da dusar kwal bayan da muka wanke kwal, sabo da haka an gurbata muhalli sosai. Amma yanzu mun kafa wata masana'anta wajen samar da wutar lantarki da dusas kwal. Daga baya kuma muna yin amfani da tokar kwal da masana'antar wutar lantarki ta samar wajen kera bulo da siminti. Ta haka muna yin amfani da dukkan abubuwa marasa amfani. Ban da wannan kuma, an kafa wani tsarin sake yin amfani da gurbataccen ruwa da aka riga aka tsabtace shi a cikin kamfaninmu, shi ya sa yanzu ba za mu fitar da gurbataccen ruwa zuwa waje ba."
A da, dusar kwal da tokar kwal abubuwa masu gurbata muhalli ne, amma yanzu bayan da aka sake yin amfani da su, ba kawai ba za su yi illa ga muhalli ba, har ma za su zama abubuwa masu amfani sosai. Sabo da kamfanin sarrafa kwal na Shenhua yake bin irin wannan salon bunkasuwa, shi ya sa ba kawai yana yin tsimin makamashi da kuma kiyaye muhalli ba, har ma ya samu karuwa cikin sauri wajen tattalin arzikinsa.
Ba kawai masana'antun jihar Mongolia ta gida suna mai da hankali kan tsimin makamashi da kiyaye muhalli ba, har ma wasu fararen hula na jihar suna dora muhimmanci kan batun. A cikin kauyen Lianfeng na birnin Baotou da ke jihar, ko wane gida ya kafa wurin samar da iskar gas, ta yadda za a iya dafa abinci da yi wa kayayyakin lambu ban ruwa ta hanyar yin amfani da iskar gas da aka samu daga wajen kashin dabbobi.
Sabo da yaduwar iskar gas, 'yan kauyen sun kirkiro sabbin kayayyaki masu yawa na yin amfani da iskar gas. Shugaban kauyen Zhang Jieping ya yi mana bayani cewa,
"Wannan shi ne kwanon dafa shinkafa, wanda ake yin amfani da iskar gas a maimakon wutar lantarki. Bayan da aka ajiye shinkafa da kuma ruwa a cikinsa, zai fara dafa shinkafa da kansa ta yin amfani da iskar gas. Ban da wannan kwanon dafa shinkafa, muna da injunan dumama daki wadanda ake yin amfani da iskar gas, ta yadda za su iya dumama daki a lokacin hunturu."
Jihar Mongolia ta gida tana arewacin kasar Sin, kuma albarkatunta suna da yawa. Shi ya sa wasu wuraren jihar suka fara yin amfani da wadannan albarkatu domin raya makamashi mai tsabta. Daga cikinsu, dimbin wuraren da ke tsakiyar jihar suna bunkasa aikin samar da wutar lantarki da karfin iska. Birnin Wulanchabu yana daya daga cikinsu. Sabo da kilomita 336 kawai tsakanin birnin da birnin Beijing, shi ya sa za a iya janyo wutar lantarki da birnin yake samarwa zuwa Beijing kai tsaye domin nuna goyon baya ga wasannin Olympics na shekara ta 2008.
Wu Yongxin, sakataren birnin ya gaya wa wakilinmu cewa, tashar samar da wutar lantarki ta SanXia ita ce tasha mafi girma wajen samar da wutar lantarki da karfin ruwa a kasar Sin yanzu, amma birnin Wulanchabu yana cikin shirin gina wata tashar Sanxia da ke sararin sama, wato yana son zama birni mafi girma wajen samar da wutar lantarki da karfin iska a kasar Sin. Kuma ya kara da cewa,
"A cikin jiharmu, ana iya samun iska a ko ina, amma birnin Wulanchabu yana da iska mafi karfi. Haka kuma birnin yana kusa da birnin Beijing, shi ya sa ana iya janyo wutar lantarki da birnin yake samarwa zuwa ko ina na jihar har Beijing a ko yaushe. Sabo da haka ina ganin cewa, shirin raya birnin Wulanchabu domin ya zama birni mafi girma wajen samar da wutar lantarki da karfin iska a kasar Sin ba wani mafarki ba ne."
Bayan da aka yi nazari a cikin shekaru kusan goma da suka gabata, yanzu kasar Mongolia ta gida ta riga ta samu wata hanyar samun dauwamammiyar bunkasuwa wajen tsimin makamashi da kuma kiyaye muhallin halittu.(Kande Gao)
|