Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-24 14:15:47    
Rahoto daga kasar Amurka ya amince da matsanancin halin da ake ciki a kasar Iraki

cri

A ran 23 ga wata, wata hukumar leken asiri ta kasar Amurka ta bayar da wani rahoto, inda aka bayyana cewa, ko da yake an kyautata halin tsaro da ake ciki a kasar Iraki tun daga watan Janairu na shekarar da muke ciki, amma gwamnatin kasar Iraki ba ta tafiyar da harkokin mulki yadda ya kamata ba, haka kuma rundunar tsaro ta Iraki ba ta iya daukan matakai da kanta ba idan babu taimakon sojojin kasar Amurka. Wannan rahoto ya ci gaba da cewa, a cikin watanni 6 zuwa 12 masu zuwa, rundunar tsaro ta Iraki ba za ta iya taka rawa sosai ba wajen kiyaye zaman lafiya a kasar.

Wannan rahoto ya nuna shakku sosai ga kwarewar gwamnatin kasar Iraki, wadda Nouri al-Maliki yake shugabanta, wajen kawar da bambancin ra'ayi a tsakanin rukunoni daban daban na addinai, da kuma cim ma burin kasar Amurka. Wannan rahoto ya fadi cewa, gwamnatin kasar Iraki ba ta samu ci gaba wajen samun sulhuntawa a fannin siyasa, haka kuma ba za ta iya samun kyakkyawar dama ba a nan gaba. Rahoton yana ganin cewa, dalilin da ya sa ba a samu babban ci gaba wajen samun sulhuntawar siyasa a Iraki ba shi ne, domin ko da yake gwamnatin Iraki ta riga ta samu goyon baya daga rukunin Shi'a, amma ba a kawar da bambancin ra'ayi a tsakanin rukunin Shi'a da na Sunni da kuma Kurdawa ba.

A majalisar dokoki ta kasar Amurka, wasu 'yan majalisa na jam'iyyar dimokuradiyya sun bukaci Maliki ya yi murabus daga mukaminsa, ban da su kuma, wasu 'yan majalisa na jam'iyyar Republikan su ma sun kai suka kan manufofin da gwamnatin Bush take gudanarwa a kasar Iraki. A ran 23 ga wata, wato lokacin da aka gabatar da wannan rahoto, wani babban 'dan majalisar dattawa Mr John Warner ya sa kaimi ga Mr Bush da ya janye wasu sojojin Amurka daga Iraki kafin bikin Christmas na bana. Mr Warner ya bayyana cewa, makasudin wannan mataki shi ne, a yi gargadi ga gwamnatin Iraki cewa, ba ta da lokaci mai yawa, zai kasance da jadawali da alkawarin da kasar Amurka ta yi wa Iraki.

Wannan rahoto kuma ya matsa wa gwamnatin Bush lamba. Wani jami'in da ba ya son fadin sunansa ya yi magana kamar haka, 'dukkan kokarin da muke yi sun zama banza, ba su taka rawa ba, ko da yake haka ne, amma ba su iya daina su ba, idan mun daina, lallai, halin da ake ciki zai kara tsanancewa.' Ban da wannan kuma, wasu jami'an fadar White Housa sun amince da cewa, ra'ayin da wannan rahoto ya samu ya fi tsanani, idan aka kwatanta shi da kimantawar White House. Wani 'dan majalisar dattawa na jam'iyyar dimokuradiyya Mr Harry Reid ya bayyana cewa, wannan rahoto ya sake tabbatar da cewa, sojojin Amurka suna cikin mawuyacin hali a yakin basasa na Iraki, shirin kara tura sojoji da Mr Bush ya gabatar, bai cim ma burin da ya yi alkawari ba a da. Wasu shugabannin jami'yyar dimokuradiyya sun bayyana cewa, za su ci gaba da tilastawa gwamnatin Bush domin ta daina yakin Iraki.

A hakika dai, kafin kwana daya da gabatar da wannan rahoto, Mr Bush ya yi wani jawabi, inda ya jaddada cewa, sojojin kasar Amurka za su samu nasara a Iraki a nan gaban ba da dadewa ba, sabo da haka Mr Bush ya bukaci jama'ar kasar Amurka kada su yarda da ra'ayin wasu mutane wai janye sojoji daga Iraki. Game da haka, kafofin watsa labaru suna ganin cewa, ba zai kasance da matukar yiyuwa ba Mr Bush ya canza manufofinsa a Iraki. Amma gwamantin Bush tana shan wahala sosai domin matsanancin halin da ake ciki a Iraki.(Danladi)