Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-23 18:28:19    
Asalin matsalar Taiwan(B)

cri

A watan Disamba na shekara ta 1978 gwamnatin Amurka ta amince da ka'idoji uku da gwamnatin kasar Sin ta gabatar yayin da ake neman kulla huldar waje tsakanin kasashen nan biyu,ka'idojin nan uku su ne Amurka ta yanke "huldar waje" dake tsakaninta da hukumomin Taiwan,da soke yarjejeniyar hadin gwiwa kan harkokin tsaro' da kuma janye sojojin Amurka daga Taiwan.A ran daya ga watan Janairu na shekara ta 1979 aka kulla huldar waje a hukunce tsakanin Sin da Amurka.Hadaddiyar sanarwa ta kulla huldar waje tsakanin Sin da Amurka ta sanar da cewa "tarayyar kasashen Amurka ta amince da gwamnatin jamhuriyar jama'ar kasar Sin a kan matsayin gwamnatin halal daya tak ta kasar Sin.Bisa haddin wannan sanarwar,mutanen Amurka na cigaba da mu'amala da mutanen Taiwan kan harkokin al'adu da cinikayya da ma na sauran fannoni da ba su shafi hukumomin gwamnati ba",gwamnatin tarayyar kasashen Amurka ta amince da matsayin kasar Sin wato Sin daya a duniya,Taiwan wani yanki ne na kasar Sin."

Abin bakin ciki shi ne bai kai watanni uku ba da aka kulla huldar waje tsakanin Sin da Amurka,kiri da muzu majalisar dokoki ta Amurka ta zartas da wata "doka game da dangantaka da Taiwan,"kuma ta fara aiki da ita bayan da shugaban kasar Amurka ya sa hannu a kai.Wannan "dokar dangantaka da Taiwan" ta karya abubuwa da dama da aka tanada cikin hadaddiyar sanarwa ta kulla huldar waje tsakanin Sin da Amuka da kuma ka'idojin da ake bi na dokokin kasa da kasa.Bisa wannan doka Gwamnatin Amurka ta ci gaba da sayarwa Taiwan da makamai da yin katsalanda cikin harkokin gida na kasar Sin da girka katanga ga hadewar Taiwan da babban yankin kasar Sin.

Domin daidaita bautn sayar da makaman da Amurka ta yi wa Taiwan,gwamnatin Sin da ta Amurka sun daddale wata yarjejeniya a ran 17 ga watan Augusta na shekara ta 1982 ta hanyar shawarwari,suka bayar da hadaddiyar sanarwa ta uku dangane da dangantaka dake tsakanin Sin da Amurka,a takaice ana kiranta "sanarwar ran 17 ga watan Augusta".A cikin sanarwar gwamnatin Amurka ta shelanta cewa Amurka ba ta nemi tafiyar da wata manufar sayarwa Taiwan da makamai cikin dogon lokaci ba,makaman da za ta sayar wa Taiwan ba su zarce makaman da ta sayarwa mata ba bisa amfaninsu da adadinsu cikin 'yan shekaru bayan kulla huldar waje tsakanin Sin da Amurka,kuma a shirye take za ta rage yawan makaman da take sayarwa Taiwan,bayan wani lokaci za a kai daidaita matsalar nan.Duk da haka cikin dogon lokaci gwamnatin Amurka ba ta aiwatar da abubuwan da aka tanada a cikin hadaddiyar sanarwa cikin tsanaki ba,ta yi ta karya abubuwan da aka tanada a cikin hadaddiyar sanarwa.Duk da haka har ma a watan Satumba na shekara ta 1992 gwamnatin Amurka ta tsaida kudurin sayar da jiragen saman yaki masu inganci 150 kirar F-16 ga Taiwan.Wannan matakin da gwamnatin Amurka ta dauka ya kara gitta katanga da hani ga bunkasa dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka da warware matsalar Taiwan.

Da haka har yanzu ba a warware matsalar Taiwan ba tukuna,gwamnatin Amurka tana da nayi nata a kan wannan batu.

"Warware matsalar Taiwan da tabbatar da hadewar kasa" wata dawainiyya ce mai tsarki ga daukacin jama'ar kasar Sin.Bayan da aka kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin,gwamnatin kasar Sin ta yi iyakacin kokarinta domin neman cika wannan dawainiyya.Muhimmiyar manufar da gwamnatin kasar Sin ke bi wajen neman warware matsalar Taiwan ita ce "hade kan kasa cikin ruwan sanyi da kasa daya da tsarin mulkin guda biyu".

Tun farkon shekarun 1950 gwamnatin kasar Sin ta yi shirin warware matsalar Taiwan cikin ruwan sanyi.A zaman kwamitin dindindin na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da aka yi a watan Mayu na shekara ta 1955,marigayi firayim minista Zhou Enlai ya bayar da ra'ayinsa cewa "wajen warware matsalar Taiwan da akwai hanyoyi biyu da mutanen kasar Sin za su yiwu su dauka,wato ta hanyar yaki ko ta hanyar zaman lafiya,bisa sharadin da zai yiwu,mutane kasar Sin sun fi so a warware matsalar Taiwan cikin ruwan sanyi.A watan Afril na shekara ta 1956,marigayi shugaba Mao Zedong ya ba da ra'ayinsa mai manufa da cewa "sulhuntarwa ta fi kome daraja" da "masu kishin kasa iyali daya" da kuma babu wanda ya ke matsayin gaba da na baya wajen kishin kasa".Duk wadannan shawarwarin da aka kawo ba a tabbatar da su ba sabo da katsalandar da kasashen ketare suka yi.