Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-22 18:28:02    
Kasar Sin ta kara karfin ba da agaji domin yaki da bala'u a shekarar bana

cri

Tun daga farkon wannan shekara, kasar Sin take gamuwa da bala'o'i da suka hada da ambaliyar ruwa da fari da girgirzar kasa, ta fi shan wahalar bala'u, in an kwatanta da shekarun baya da suka wuce. Ya zuwa yanzu dai, bala'u daga indallahi iri daban daban sun shafi mutane kimanin miliyan 310, sun haddasa hasarar kudin Sin yuan biliyan 126 ko fiye kai tsaye ta fuskar tattalin arziki.

Ran 22 ga wata, a gun taron manema labaru da ofishin yada labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya, ministan kula da harkokin jama'a ta kasar Sin malam Li Xueju ya bayyana cewa, gwamnatin Sin ta dora muhimmanci sosai kan rage aukuwar bala'u da kuma ba da agaji. Ma'aikatar harkokin jama'a ta kasar Sin ta karfafa matakan a-zo-a-gani domin raya tsarin ko-ta-kwana na yaki da bala'u daga indallahi, ta kuma kula da halin da wurare daban daban na kasar ke ciki a fannin sauye-sauyen bala'u. Sa'an nan kuma, ta aiwatar da 'shirin ko-ta-kwana na ba da agaji domin yaki da bala'u daga indallahi' cikin lokaci bisa sauye-sauyen bala'u, ta kuma ware kudade da kayayyakin agaji cikin lokaci, ta jagoranci hukumomin wuraren kasar da su yaki da bala'un da kuma ba da agaji. Malam Li ya ce,'Ma'aikatarmu ta aiwatar da shirin ko-ta-kwana har sau 41 a shekarar da muke ciki. Mun kafa tsarin ba da agaji cikin gaggawa don tabbatar da ganin cewa, masu fama da bala'u suna da isasshen abinci da tufafi da wurin kwana da ruwan sha mai tsabta, suna iya samun magani cikin lokaci in sun kamu da ciwo. Ban da wannan kuma, kasarmu ta kafa tsarin ba da agaji ga masu fama da bala'u bayan aukuwar bala'u, ta haka za ta warware matsalolin sake gina gidaje da ba da agaji ta fuskar zaman rayuwa.'

Malam Li ya kara da cewa, aukuwar bala'u ke da wuya, sai hukumomin kasar Sin na matakai daban daban da wadanda abin ya shafa sun dauki matakai nan da nan, suna taimakawa juna wajen gudanar da aiki bisa tunanin 'tafiyar da ayyuka domin bauta wa masu fama da bala'i'. Hakan na taka muhimmiyar rawa wajen rage yawan mutuwa da hasarar da bala'u suka haddasa.

An yi karin bayanin cewa, a shekarar bana, ma'aikatar harkokin jama'a ta kasar Sin ta tura kungiyoyin ayyukan ba da agaji guda 41 zuwa wurare masu fama da bala'i daya bayan daya, ta kuma yi jigilar tantuna fiye da dubu 40 zuwa lardunan da ke fi fama da bala'u domin ba da agaji, ta haka ta samar da wuraren kwana na wucin gadi ga fararen hula da aka tsugunar da su yadda ya kamata. Dadin dadawa kuma, baitulmalin gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta kebe kudin ba da agaji da yawansa ya wuce kudin Sin yuan biliyan 11.5. Gwamnatin Sin ta kuma daga ma'aunin alawus a fannin sake gina gidaje bayan rushewar gidaje, ta daga ma'aunin alawus wajen yin kwaskwarima kan gidaje bayan girgizar kasa. Ban da wannan kuma, ta daga wa fararen hula ma'aunin alawus ta fuskar zaman rayuwa a lokacin hunturu da bazara. Dukkan wadannan matakai sun warware matsalolin da masu fama da bala'u ke fuskanta a fannin zaman rayuwa, sun tabbatar da zaman rayuwar wadannan mutane.

Saboda kasar Sin ta kafa cikakken tsarin ba da agaji bayan aukuwar bala'u, ta kara goyon bayan ayyukan ba da agaji, sa'an nan kuma, ta kara zuba kudi kan kyautata muhallin koguna da muhimman ayyuka a shekarun nan da suka wuce, ta kuma kyautata ingancin gidajen fararen hula, shi ya sa karfin kasar Sin wajen magance ambaliyar ruwa ya sami kyautatuwa a bayyane a bana. Malam Li ya ce,'Yawan masu shan wahalar bala'u ya ragu da kashi 9.4 cikin kashi dari a wannan shekara, bisa na shekarar bara, haka kuma, yawan mutuwa ya ragu da kashi 34.8 cikin kashi dari. Ko da yake kasarmu ta fi gamuwa da bala'u a wannan shekara, amma don me irin wadannan adadi 2 sun ragu bisa na shekarar bara? A ganina, dalilin da ya sa haka shi ne domin a shekarun nan da suka wuce, kasarmu ta kara kyautata muhallin koguna da muhimman ayyuka, ta kuma karfafa karfin magance ambaliyar ruwa.'

Baya ga kara goyon bayan ayyukan ba da agaji, kasar Sin ta kara sa ido kan yin amfani da kudin ba da agaji da kyautar kudin da zaman al'ummar kasa ke bayarwa. Malam Li ya ci gaba da cewa, kasar Sin ta dauki matakai da yawa domin tabbatar da ganin dukkan masu fama da bala'u za su ci gajiyar wadannan kudade.(Tasallah)