Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-22 10:39:00    
Kungiyar wakilan `yan wasan kasar Sin tana yin kokari domin shiga taron wasannin Olimpic na Beijing

cri

Masu sauraro,kamar yadda kuka sani,a kullum kungiyar wakilan `yan wasan kasa mai shirya taron wasannin Olimpic ta fi jawo hankulan mutanen kasashen duniya.Saboda `yan wasan kasar Sin sun taba samu babban sakamako a gun taron wasannin Olimpic na Athens,shi ya sa wasu kwararrun mutanen fannin wasannin motsa jikin duniya suna ganin cewa,ko shakka babu `yan wasan kasar Sin za su samu sakamako mai faranta ran mutane a gun taron wasannin Olimpic da za a yi a birnin Beijing a shekarar 2008,haka kuma kila ne za su samu lambobin zinariya mafiya yawa.Amma,jami`an kula da wasannin motsa jiki na kasar Sin ba su yarda da wannan ba.Kwanakin baya ba da dadewa ba,mataimakin shugaban babbar hukumar kula da wasannin motsa jiki ta kasar Sin Cui Dalin ya bayyana cewa,nufin kungiyar wakilan `yan wasan kasar Sin a gun taron wasannin Olimpic na Beijing shi ne domin samun sakamako mai kyau a cikin kungiyoyin wakilan `yan wasa na rukuni na biyu wato a bayan kungiyoyin rukuni na farko wadanda za su fi nagari.a cikin shirinmu na yau,bari mu yi muku bayani kan wannan.

Tun bayan da kungiyar wakilan `yan wasan kasar Sin ta sake shiga taron wasannin Olimpic na yanayin zafi na shekarar 1984,a kullum tana samun sakamako mai faranta ran mutane,musamman a bayan taron wasannin Olimpic na Barcelona na shekarar 1992.A shekarar 2004,a gun taron wasannin Olimpic na Athens,gaba daya kungiyar wakilan `yan wasan kasar Sin ta samu lambobin zinariya 32,ta samu zama ta biyu a bayan kungiyar kasar Amurka wadda ta samu lambobin zinariya 36.Tun daga wancen lokaci,mutane da yawan gaske suna ganin cewa,a gun taron wasannin Olimpic da mutanen kasar Sin za su shirya a birnin Beijing a shekarar 2008,sakamakon da kungiyar kasar Sin za ta samu zai fi na da.Wasu kuwa sun yi nuni da cewa,kasar Sin za ta zarce kasar Amurka wato lambobin zinariya da za ta samu za su fi na kasar Amurka yawa.Duk da haka,mutanen fannin wasannin motsa jiki na kasar Sin ba su yarda da wannan ra`ayi ba.Game da wannan,mataimakin shugaban babbar hukumar kula da wasannin motsa jiki ta kasar Sin Cui Dalin ya bayyana cewa,hakikanin halin da ake ciki yanzu ba haka ba ne.Ya ce:  `Cikakken karfin wasannin motsa jikinmu bai kai na kasar Amurka da kasar Rasha ba,ban da wannan kuma wasu kasashe kamarsu kasar Jamus da kasar Australia da kasar Faransa da kasar Japan da kasar Korea ta kudu da sauransu su ma suna da karfi.Idan ana mayar da kasar Amurka da kasar Rasha a matsayin rukuni na farko,to,kamata ya yi kasarmu da sauran kasashen da muka ambata a sama muna cikin rukuni na biyu,nufinmu a gun taron wasannin Olimpic na Beijing shi ne mu yi kokari domin zama zakara a cikin rukuni na biyu.`

A hakika dai,ma`aunin karfin takara ba yawan lambobin zinariya ba ne,kamata ya yi a mai da hankali kan dukkan lambobin yabo da aka samu.Kazalika,kungiyar kasar Sin tana fuskantar wasu matsaloli mafiya tsanani.Cui Dalin ya ce,wasu wasanninmu suna fuskantar kalubale,wasu kuwa ba su da karfi.Ban da wannan kuma,a gun taron wasannin Olimpic na Beijing,za a soke wasu gasanni kamarsu wasan harbe-harbe da wasan takobi,duk wadannan za su kawo tasiri ga kasar Sin wajen samun lambobin yabo saboda `yan wasan kasar Sin sun taba samu sakamako mai kyau a cikin wadannan gasanni.

Cui Dalin ya bayyana cewa,lambar yabo ba abu mafi muhimmanci ba ce,`yan wasan kasar Sin suna son nunawa kasashen duniya sauran halaye.Ya ce:  `Nufinmu ba lambobin yabo ba ne,abu mafi muhimmanci gare mu shi ne nuna wa kasashen duniya halin wasannin Olimpic da halin wasannin motsa jikin kasar Sin da kuma halin `yan wasan kasar Sin.Ban da wannan kuma,za mu sanya matukar kokari domin neman samun lambobin yabo.A karshe dai,muna son kara karfafa cudanya tsakaninmu da sauran kasashe.Daga baya kuma muna so mu yada wasannin motsa jiki a duk fadin kasar.`

Cui Dalin ya hakake cewa,jama`ar kasar Sin su ma ba za su mai da hankali kan yawan lambobin yabo ba kawai.Ya ce:  `Muddin dai `yan wasanmu sun yi iyakacin kokarinsu,to,jama`ar kasar Sin za su gamsu da kokarinsu,kuma za su gode wa kokarin da suka yi domin kasarmu.Ana iya cewa,yawan lambar yabo ba ma`auni daya kadai ba ne.`

To,jama`a masu sauraro,karshen shirinmu na yau ke nan,ni Jamila da na gabatar nake cewa,ku zama lafiya,sai makon gobe war haka idan Allah ya kai mu.(Jamila Zhou)