Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-22 10:37:30    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (15/08-21/08)

cri

Ran 18 ga wata,an rufe zama na 24 na taron wasannin daliban jami`o`in kasashen duniya na yanayin zafi a birnin Bangkok na kasar Thailand.A gun taron da aka shirya,kungiyar wakilan kasar Sin ta samu lambobin zinariya 33 da na azurfa 30 da kuma na tagulla 27,wato lambobin zinariya da ta samu sun fi yawa,kungiyar wakilan kasar Rasha ta samu zama ta biyu a bayanta,kungiyar wakilan kasar Ukraine kuwa ta samu zama ta uku.Gaba daya `yan wasa da suka zo daga kasashe da shiyoyyi 156 sun halarci gasannin da aka shirya domin neman samun lambobin zinariya 236 na manyan wasanni 15.Za a yi zama na 25 na taron wasannin daliban jami`o`in kasashen duniya na yanayin zafi a birnin Belgrade na Serbia a shekarar 2009.

Ran 13 ga wata,an rufe gasar wasanni uku na wasan tseren doki na duniya da aka shafe kwanaki uku ana yinta a yankin musamman na kasar Sin wato Hongkong,ana kiran gasar nan da sunan `Beijing mai sa`a`.`Dan wasa daga kasar Jamus Frank Ostholt ya zama zakara tare da dokin gasarsa mai suna `After The Battle`.

Ran 19 ga wata,an rufe gasar cin kofin duniya na wasan kwallon badminton na shekarar 2007 a birnin Kuala Lumpur na kasar Maylasia.A gun gasannin da aka shirya,kungiyar kasar Sin ta samu zama ta farko da lambobi na kan gaba uku wato `dan wasa daga kasar Sin Lin Dan ya lashe `dan wasa daga kasar Indonesia Sony Dwi Kuncoro ya zama zakaran maza,`yar wasa daga kasar Sin Zhu Lin ta lashe `yar wasa daga Hongkong Wang Chen ta zama zakarar mata,ban da wannan kuma `yan wasan kasar Sin Yang Wei da Zhang Jiewen sun samu zama ta farko ta gasar dake tsakanin mata biyu biyu. (Jamila zhou)