Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-21 17:06:48    
Titin Guanqian a birnin Suzhou na lardin Jiangsu

cri

Titin Guanqian yana birnin Suzhou na lardin Jiangsu. Ma'anar titin ita ce wannan titi yana gaban wani gidan ibada. Ma'anar Guan a bakin Sinawa ita ce gidan ibada, Qian kuwa ita ce a gaban wani abu. Titin Guanqian yana gaban gidan ibada na Xuanmiao, wanda ke tsakiyar titin, sa'an nan kuma, shi wani mashahurin wuri ne da masu bin addin Taoism su kan kai masa ziyara.

A gefuna 2 na titin Guanqian, akwai dimbin kantuna da shaguna iri daban daban da dakunan cin abinci, wadanda suka iya biyan bukatun mutane daga fannoni daban daban. Tarihin titin ya wuce shekaru dubu 1. Tsawonsa kuma ya kai misalin mita 760, ya hada da bangare na gabas da na tsakiya da na yamma.

A bangaren gabas na titin, ana adane da yawancin gine-ginen zamanin da masu muhimmanci a tarihi, kamar su daddadun kantuna da shaguna na gargajiya masu dimbin yawa, wadanda ke mallakar shahararrun tambarin kasuwanci. A bangaren tsakiyar titin, an sami gidan ibada na Xuanmiao. Sa'an nan kuma, kantuna masu kawa suna mamaye da bangaren yamma na titin

Ban da wannan kuma, an kebe wani shiyya a kan titin Guanqian domin sayar da kayayyakin fasaha da kayayyakin kananan sana'o'i. Wata rumfa mai benaye 2 da aka gina a zamanin daular Tang a tsakanin shekarar 618 zuwa ta 907 ta sayar da kayayyakin fasaha na gargajiya da yawa, wadanda suka hada da abubuwan sassaka da aka yi da tubali da duwatsu da kuma abubuwan fenti da lu'ulu'u da zane-zane da kuma kayayyakin daki irin na zamanin daular Ming da Qing wato tsakanin shekarar 1368 zuwa ta 1912. A kan bene na biyu na rumfar, wani ma'adadin hotunan zane yana nuna zane-zanen da aka yi da mai da mutum-mutumin saka na zamanin yanzu. Ban da wannan kuma, ma'adainin nan ya kan nuna wasannin kwaikwayo irin na gargajiya da zane-zane irin na gargajiya da kuma kayayyakin fasaha irin na kasar Sin kullum