Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-21 17:00:23    
Shan nonon iyaye mata zai iya ba da taimako wajen rage yiyuwar yaduwar cutar kanjamau tsakanin iyaye mata da jariransu

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai farin jini wato "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". A cikin shirinmu na yau, da farko za mu yi muku wani bayani kan cewa, shan nonon iyaye mata zai iya ba da taimako wajen rage yiyuwar yaduwar cutar kanjamau tsakanin iyaye mata da jariransu, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani kan cewa, birnin Baoding na kasar Sin yana dukufa kan raya makamashin zafin rana.

Bayan da masu ilmin kimiyya na kasar Afirka ta Kudu suka yi nazari, sun gano cewa, a cikin jariran da shekarunsu bai zarce watanni shida ba, game da wadanda suka sha nonon iyaye mata kawai, yiyuwar kamuwa da cutar kanjamau daga iyayensu mata kadan ce sosai, idan an kwatanta su da wadanda suka sha garin madara.

Bisa wani bayanin da jaridar kasar Kenya ta bayar a ran 1 ga watan Afril na shekarar da muke ciki, an ce, masu ilmin kimiyya na cibiyar nazarin kiwon lafiya da yawan mutane ta Afirka sun bayyana cewa, game da jariran da shekarunsu ya kai daga makwanni shida zuwa watanni shida, idan sun sha nonon iyayensu mata kawai, to yiyuwar kamuwa da cutar kanjamau daga iyayensu mata za ta kai kashi 4 cikin dari kawai, amma game da jariran da suka sha garin madara da kuma nonon dabbobi, yiyuwar kamuwa da cutar za ta ninka sau daya, wato za ta kai kashi 8 cikin dari, haka kuma idan jarirai suna cin sauran abinci ban da nono, to yiyuwar kamuwa da cutar za ta ninka kusan sau 10.

Masu ilmin kimiyya sun yi bayani cewa, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da abinci ya kan kunshi sinadari mai gina jiki da yawa, wadanda suke iya lallata fatar da ke cikin cikin jarirai, ta haka kwayoyin cutar kanjamau za su fi saukin shiga ciki.

Ban da wannan kuma sun bayyana cewa, a kasashe masu ci gaba, sabo da ana yin amfani da dabarar yaki da sinadarin retrovirus wajen shawo kan cutar kanjamau, da samar da abinci ga jarirai kamar yadda ya kamata, da kuma ba da tabbacin jiyya, shi ya sa yawan jariran da ke kamuwa da kwayoyin cutar kanjamau daga iyayensu mata ya ragu daga kashi 25 zuwa kashi 2 cikin dari. Amma ba a yada wadannan dabaru a kasashe masu tasowa ba, shi ya sa masu ilmin kimiyya suna ganin cewa, ya fi kyau a kara yada dabarar samar da nonon iyaye mata a kasashe masu tasowa wajen shawo kan yaduwar cutar kanjamau.

Jama'a masu sauraro, yanzu sai ku huta kadan, bayan haka kuma za mu karanta muku wani bayani kan aikin raya makamashin da ake samu daga zafin rana da ake tafiyar a kasar Sin. Yanzu, an dukufa kan raya makamashin karfin iska da na zafin rana da na zafin kasa da dai sauran sabbin makamashi a wurare daban daban na kasar Sin domin canja halin da ake ciki wajen dogaro da makamashin gargajiya kamar kwal da man fetur da iskar gas. Birnin Baoding na lardin Hebei da ke arewacin kasar Sin yana daya daga cikinsu, inda ake yin kokari wajen mayar da birnin da ya zama wani birnin da ke yin amfani da makamashin zafin rana. To, a cikin shirinmu na yau, za mu leka birnin Baoding domin ganin yadda yake raya fasahar yin amfani da makamashin zafin rana.