Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-20 20:22:08    
Wasu labaru game da jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta ta kasar Sin

cri

Wani labarin farko shi ne jimlar GDP ta jihar Mongolia ta gida ta kasar Sin ta ninka sau 196 a cikin shekaru 60 da suka gabata

Jimlar kudaden da jihar Mongolia ta gida ta kasar Sin ta samu wajen samar da kayayyaki wato GDP ta ninka har sau 196 a cikin shekaru 60 da suka gabata bayan da jihar ta samu 'yancin kai.

Shugaban jihar Mongolia ta gida Yang Jing ya yi wannan kalami ne a gun taron manema labarai da aka shirya a ran 25 ga wata a birnin Beijing.

Kuma Mr. Yang ya bayyana cewa, lokacin da ake raya tattalin arziki na jihar, ana dukufa kan kyautata zaman jama'arta, da kuma tafiyar da ayyukan da ke amfana wa mutane masu fama da talauci. Daga shekara ta 2001 zuwa shekara ta 2005 kawai, manoma da makiyaya fiye da dubu 900 na jihar da suka fice daga cikin kangin talauci, kuma nazaunan birane da garuruwa fiye da dubu 700 sun samu kudaden ba da tabbacin zaman rayuwa mafi kankanta. Ban da wannan kuma, an warware matsalolin samun guraban aikin yi ga dukkan iyalan da ba su da aikin yi a da, da samar da kudin karatu ga dalibai masu fama da talauci, da samun ruwan sha mai tsabta ga manoma da makiyaya, da kuma kyautata sharuddan samar da amfanin gona da zaman rayuwa na manoma da makiyaya.

Wabi labari daban shi ne jihar Mongoliya ta gida tana kokarin kyautata muhallin duniya

Bayan da ta yi kokari har na tsawon wasu shekaru, fadin filin itatuwa da ciyayi da aka dasa a jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta ta kasar Sin ya samu karuwa. Fadin hamada ya ragu fiye da kadada miliyan 1.3. Sabo da haka, muhallin duniya na jihar ya samu kyautatuwa sosai. Yanzu ana samun raguwar kwararowar hamada a yankin.

An bayyana cewa, jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta tana kiyaye muhalli ne ta hanyoyin mayar da gonaki da su zama gandun daji tare da mayar da filayen kiwo da su zama filayen ciyayi. Bugu da kari kuma, gwamnatin jihar tana sa kaimi wajen raya sabbin sana'o'i iri iri domin canjin tsarin kiwo da rage yawan dabbobin da ake kiwo a kowace ektar filin ciyayi. Sabo da haka, za a iya cimma burin kyautata muhalli da kuma raya tattalin arziki tare, jam'a za su iya samun moriya daga cigaban tattalin arziki.

Domin wadannan hanyoyin kyautata muhalli suna dacewa da babbar moriyar jama'a, yanzu yawan manoma da makiyaya wadanda suke neman mayar da gonaki da filayen kiwo da su zama gandun daji da filayen ciyayi yana ta karuwa. (Sanusi Chen)