Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-17 15:45:09    
Ziyara a makarantar wasan kwallon kafa ta Qinhuangdao

cri

Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, birane guda shida wadanda suke bada taimako ga gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing,ko wanensu yana da nasa al'adun wasan motsa jiki na musamman. Birnin Qinhuangdao yana daya daga cikinsu, inda ke da wata makaranta daya tilo ta wasan kwallon kafa a matakin kasa. Kananan yara da dama masu kishin wasan kwallon kafa suna neman cimma kyakkyawan burinsu a nan, inda wasu matasa da kananan yara mata suka dauke shi tamkar 'wuri mai tsarki'.

Wani karamin yaro mai suna Xiao Yanan ya fadi cewa: " Na soma sha'awar wasan kwallon kafa ne tun ina da shekaru shida da haihuwa domin a can lokacin babana shi ma yana buga kwallon kafa. A lokacin da yake buga kwallon, na nuna sha'awa sosai ga wancan kwallon, na je wuri da sauri inda kwallon yake. Yanzu ni kyafti ne a filin gasa. Na san cewa, a matsayin wani kyafti, kamata ya yi na nuna saukin kai wajen warware matsalolin da mukan gamu da su a filin gasa. Kuma dole ne mu buga kwallon kafa daidai bisa dabarun da mai koyar da 'yan wasa ya yi ko da wani lokaci mun kasa jefa kwallo cikin raga ta abokan karonmu''.

Abin da kuke ji ne daga bakin wani yaro da ake kira Xiao Yanan mai shekaru 13 kawai da haihuwa. Wannan yaro yana koyon fasahar buga kwallon kafa a wannan makaranta ne cikin shekaru da dama. Da yake ya yi wayo sosai da nuna jan halin zuciya wajen buga kwallo, shi ya sa ya yi wa 'yan ajinsa fintinkau. Za a shigar da shi cikin kungiyar wasan kwallon kafa ta kananan yara na kasar Sin.

Malama Xue Liyan, mataimakiyar daraktan ofishin bada ilmin al'adu na makarantar wasan kwallon kafa ta kasar Sin ta yaba wa Xiao Yanan a kan cewa yakan buga kwallo ne da kwakwalwa. Ta kuma ce, lallai wasan kwallon kafa ya haifar da kyakkyawar halayya ga wadannan kananan yara, wadanda suke da wayo da kuma mayar da martani cikin hanzari wajen buga kwallo yayin da suke gayyar kokari wajen nuna karfin wani rukuni. Game da wadannan kananan yara dai, babu wahalar tuntubarsu.

Wadannan 'yan makaranta ,wasu da dama daga cikinsu sun dade rabo da ganin iyayensu bayan da suka zo nan makarantar. To, ba abin mamaki ba ne sukan tuna da ubanninsu da kuma iyayensu. Amma, malamai da masu koyar da 'yan wasa na wannan makaranta suna kula da wadannan kananan yara kamar yadda ubanninsu da kuma iyayensu suka yi. Saboda haka ne, wadannan yara sun saba da zaman makarantar tun da wuri.

Domin tabbatar da samun kyakkyawan ingancin aikin koyarwa, makarantar wasan kwallon kafa ta kasar Sin ta dauki dimbin nagartattun masu koyar da 'yan wasa na gida da na waje bisa kwangila don su horar da wadannan kananan yara a fannin wasan kwallon kafa ta tsararriyar hanya. Ban da wannan kuma, makarantar ta kan gayyaci wasu shahararrun kwararru a fannin wasan kwallon kafa na kasa da kasa ga zuwan nan domin bada darussa, ta yadda 'yan makarantar za su kara samun ilmi a fannin halayen musamman na fasaha da daburun buga kwallo. Dadin dadawa, jami'an makarantar sukan tura 'yan makarantar don su shiga gasanni iri daban-daban na gida da na waje, ta yadda 'yan makarantar za su kara samun fasahohi wajen yin gasa ta zahiri.

Da yake gwamnatin birnin Qinhuangdao ya dauki nauyin gudanar da gasanni sau 11 na wasan kwallon kafa na taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008, shi ya sa makarantar wasan kwallo kafa ta kasar Sin dake nan birnin ta yi gyaran fuska sosai don ta zama sabuwa ful. Lallai abun ya sosa zuciyar kananan yara na wannan makaranta saboda sun samu damar kallon gasanni masu ban sha'awa na wasan kwallon kafa na taron wasannin Olympic.

An labarta cewa, a cikin shekaru biyu da suka gabata, bangarorin da abin ya shafa sun zuba kudin Renminbi Yuan miliyan dari da hamsin don gyaran ginin makarantar wasan kwallon kafa ta kasar Sin. A lokacin taron wasannin Olympic na Beijing, za a mayar da filin wasan kwallon kafa na wannan makaranta don ya zama filin horaswa na kungiyoyin wasan kwallon kafa daban daban da za su zo nan birnin Qinhuangdao don halartar gasanni. Yanzu, kananan 'yan makarantar masu yawan gaske suna alla-alla wajen zama masu aikin sa kai na taron gasannin. Wani karamin dan makaranta ya fada wa wakiliyarmu cewa : ' Ina so in tafi filin gasa kuma ina so in yi musayar rigar wasan kwallo tare da 'yan wasa taurari in na samu dama'.(Sani Wang )