Bayan yakin duniya na biyu,an mayar da Taiwan ga kasar Sin bisa dokoki ko a zahir.Dalilin da ya sa aka sami matsalar Taiwan shi ne Jam'iyyar Kuomintang ta kasar Sin ta tayar da yakin basasa daga baya,abu mafi muhimmanci shi ne kasashen waje sun sa hannu a ciki.
A lokacin yaki da sojoji mahara japanawa a kasar Sin,Jam'iyyar Kuomintang ta hada kanta da Jam'iyyar kwaminis ta Sin wajen yaki da sojoji mahara japannawa suka murkushe hare haren da sojoji maharan Japannawa suka kai wa kasar Sin.Bayan da aka samu nasarar yakin,bisa daurin gindi na Amurka,rukunin jam'iyyar Kuomintang wanda Jiang Kai-shek ya jagoranta ya tayar da yakin basasa.Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ta ja ragamar mutanen Sin wajen neman yantar da kasa cikin shekaru uku da 'yan kai da suka shude,daga baya aka hambarar da gwamnatin "Jamhuriyar kasar Sin" ta Jam'iyyar Kuomintang wadda ta yi gayyar kokarin mai da agogon baya har ma mutanen kabilun kasar Sin suka yi watsi da ita.A ran daya ga watan Oktoba aka kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin wadda gwamnatinta ta kasance gwamnatin halal daya tak ta kasar Sin baki daya.Wasu sojoji da jami'an rukunin jam'iyyar Kuomintang sun ja da baya sun tsugune a Taiwan,bisa daurin gingi na gwamnatin Amurka,sai bangarori biyu na zirin teku na Taiwan a rabe suke.
Bayan yakin duniya na biyu,bisa yanayin jayayya tsakanin sansanoni biyu na Gabas da Yamma da ba sa ga maciji da juna a wancan zamani,gwamnatin Amurka ta yi kome bisa shirinta na duniya da kuma kare moriyar kasarta ta yi matukar kokarin samar da kudade da makamai har ma da tura sojoji domin taimakawa rukunin Jam'iyyar Kuomintang wajen yin yakin basasa duk domin neman murkushe jam'iyyar Kwaminis ta Sin,duk da haka gwamnatin Amurka ba ta cimma burin da take fata ba daga bisani.
Bayan da aka kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin,gwamnatin Amurka ta bi manufar kebantar da kasar Sin da kuma yi mata tarnaki.Bayan yakin Koriya ya barke Amurka ta yi katsalandan din soja kan harkokin gida na kasar Sin dadngane da bangarori biyu na zirin teku na Taiwan.A shekara ta 1950 Amurka ta tura jerin gwanon jiragen ruwan yaki na bakwai zuwa zirin tekun Taiwan,ta kuma tsugunar da rukunin jiragen saman yaki na 13 na Amurka a Taiwan.A watan Disamba na shekara ta 1954 Amurka da hukumomin Taiwan sun kulla "yarjejeniyar hadin gwiwa kan harkokin tsaro",ta haka ta mai da lardin Taiwan na kasar Sin a karkashin garkuwar Amurka.Gwamnatin Amurka ta cigaba da bin manufartar kuskure na tsolma bakinta cikin harkokin gida na kasar Sin.Wannan ya haddasa halin ja-in-ja mai tsananni a yankin zirin teku na Taiwan cikin dogon lokaci,daga nan matsalar Taiwan ta zama muhimmin batun da kasar Sin da Amurka suke gardama a kai.
Tare da sauye sauyen yanayin duniya da bunkasuwar da sabuwar kasar Sin ta samu,Amurka ta fara daidaita manufarta kan kasar Sin,dangantakar dake tsakanin kasashen nan biyu Sin da Amurka ta fara sauyi.A watan Oktoba na shekara ta 1971,aka zartas da kuduri mai lamba 2758 a babban zauren taron majalisar dinkin duniya a karo na 28 wanda a ciki a maido duk halalen iko a majalisar dinkin duniya ga jamhuriyar jama'ar kasar Sin kuma aka kori "wakilin" hukumomin Taiwan.A watan Fabrairu na shekara ta 1972,shugaban kasar Amurka Nixion ya kai ziyara a kasar Sin,aka bayar da hadaddiyar sanarwa tsakanin Sin da Amurka a birnin Shanghai.Sanarwar ta jaddada cewa "Bangaren Amurka ta ba da sanarwar cewa Amurka ta fahimci haka: a ganin daukacin mutane dake gabobi biyu na zirin tekun Taiwan da akwai Sin daya a duniya,Taiwan wani yanki ne na kasar Sin.Gwamnatin Amurka ba ta da ra'ayi na dabam kan wannan matsayin da aka dauka." (Ali)
|