Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-15 16:47:00    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (09/08-15/08)

cri
Da farko dai, ga wasu labaru game da taron wasannin Olympic da za a yi a nan Beijing a shekara mai zuwa. Ran 8 ga watan Agusta, rana ce da aka rage sauran shekara guda da bude taron wasannin Olympic na Beijing. A wannan rana, an shirya bukukuwa iri daban daban a wurare daban daban na kasar Sin domin murnar wannan muhimmiyar rana. A matsayin muhimmin bangare na bukukuwan taya murna, a ran nan da dare, shugaba Jacques Rogge na kwamitin wasan Olympic na kasa da kasa ya aika da takardun gayyata da kansa a babban filin Tian'anmen a Beijing, domin gayyatar dukkan kwamitin wasan Olympic na kasashe mambobin kwamitin wasan Olympic na kasa da kasa da su aika da 'yan wasansu zuwa taron wasannin Olympic na Beijing a shekara mai zuwa.

Ban da wannan kuma, tun daga ran 7 zuwa ran 9 ga wata, an yi taron shugabannin tawagan wakilan taron wasannin Olympic na lokacin zafi na karo na 29 a nan Beijing. A lokacin taron, shugabannin tawagan wakilan taron wasannin Olympic da suka zo daga kwamitocin wasan Olympic na kasashe 205 mambobin kwamitin wasan Olympic na kasa da kasa sun saurari rahoton da kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya gabatar game da ci gaban ayyukan share fage kan taron wasannin Olympic na Beijing, sun kuma kira tarurukan ayyuka na musamman kan batutuwan da abin ya shafa.

Ran 8 ga wata, a birnin Bangkok, hedkwatar kasar Thailand, an bude taron wasannin motsa jiki na dalibai a karo na 24. 'Yan wasa dalibai kusan dubu goma da suka zo daga kasashe da yankuna 156 sun halarci wannan taron wasannin motsa jiki. Suna karawa da juna domin neman samun lambobin zinariya 236 a cikin manyan gasanni 15. Kasar Sin ta aika da 'yan wasa 286 da su shiga manyan gasanni 13. Za a kammala taron wasannin motsa jiki a wannan karo a ran 18 ga wata.

Ran 10 ga wata, kwamitin wasan Olympic na kasa da kasa ya gabatar da ayyukan neman samun damar shirya taron wasannin Olympic na matasa na lokacin zafi na shekara ta 2010 a karo na farko. Tun daga ran 10 zuwa ran 31 ga wannan wata, kwamitocin wasan Olympic na kasashe da yankuna za su mika rahoto ga kwamitin wasan Olympic na kasa da kasa kan sunayen biranen da ke neman samun irin wannan dama. Ran 26 ga watan Oktoba wadannan birane za su gabatar da rahoton neman samun damar shirya taron wasannin Olympic na matasa. A karshen watan Febrairu na shekara mai zuwa kwamitin wasan Olympic na kasa da kasa zai yanke sharawa kan wane birni zai shirya taron wasannin Olympic na matasa na shekarar 2010 a karo na farko.(Tasallah)