Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-14 15:19:29    
Ziyarar Hu Jingtao a tsakiyar Asiya

cri

A ranar 14 ga wannan wata, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya tashi daga nan birnin Beijing don soma ziyararsa a tsakiyar Asiya. A gun ziyararsa ta kwanaki biyar, Mr Hu Jintao zai kai ziyarar aiki a kasar Kirghistan zai kuma halarci taron koli na shugabannin kungiyar hada kai ta Shanghai , sa'annan kuma zai je ganamma idonsa rawar dajin da kungiyar hada kai ta Shanghai ta shirya don yaki da ta'addanci, haka kuma zai kai ziyarar aiki a kasar Kazakhstan. wani jami'in ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ya bayyana cewa, ziyarar da Hu Jintao ke yi a wannan gami a tsakiyar Asiya wani aiki ne daban  mai muhimmanci da kasar Sin ke yi a cikin shekarar da muke ciki, hadin guiwar da kasar Sin take yi a tsakaninta da kasashe daban daban da ke yin abuta da ita kuma makwabtaka da ita a shiyyar tsakiyar Asiya da kuma samun bunkasuwarsu gaba daya na da ma'ana mai muhimmanci tare da mai yakini sosai.

A ranar 14 ga wannan wata, Mr Hu Jintao ya sauka birnin Bishkek, hedkwatar kasar Kirghstan, sa'annan kuma zai kai ziyara a kasar a karo na farko. Wannan ya zama na farko da Mr Hu Jintao ya kai ziyarar aiki a kasar. Mun sami labarin cewa, Mr Hu Jintao zai yi shawarwari a jere da shugaban kasar Kirghistan da sauran shugabannin kasar, bangarorin biyu za su rattaba hannu kan yarjejeniyoyin hadin guiwa da suke da nasaba da siyasa da tattalin arziki da cinikayya da noma da ba da ilmi da sauran fannoni. Kwanan baya, lokacin da mai ba da shawara ga ministan harkokin waje na kasar Sin Li Hui ya karbi ziyarar da manema labaru suka yi masa, ya bayyana cewa, yana da imani sosai ga ziyarar da Hu Jintao zai yi a kasar Kirghistan, ya ce, lokacin ziyarar ya yi daidai da ranar cika shekaru 15 da kulla huldar jakadanci a tsakanin kasar Sin da kasar Kirghistan, sa'anan kuma ya yi daidai da lokacin cika shekaru 5 da aka rattaba hannu kan yarjejeniyar sada zumunta a kasashen Sin da Kirghistan ,ziyarar na da ma'ana mai muhimmanci sosai a tarihi wajen sa kaimi ga kara raya huldar da ke tsakanin kasashen biyu daga dukkan fannoni.

A ranar 16 ga wannan wata, a birnin Bishkek, za a kira taron koli na shugabannin kungiyar hadin kai ta Shanghai.

Taron zai zama wani kasaitaccen taro, ban da Hu Jintao da sauran shugabannin kasashen da ke cikin kungiyar hadin kai ta Shanghai da za su halarci taron, shugabannin kasashe 'yan kallo na kungiyar, wato shugaban kasar Mongoliya da na Iran da ministan harkokin waje na kasar Pakistan da na Indiya za su halarci taron. Ban da wannan kuma, shugaban kasar Afghanistan da na Turkmenistan da mataimakin sakatare janar na Majalisar Dinkin duniya Lynn Pascoe za su halarci taron bisa matsayinsu na bakin kasar da ke shugabancin taron. In lokacin ya yi, shugabannin kasashen da ke cikin kungiyar hadin kai ta Shanghai za su rattaba hannu kan takardu mafi muhimmanci a jere, daga cikinsu, da akwai wata yarjejeniyar sada zumunta a tsakanin kasashen da ke makwabtaka da juna kuma abuta da juna na kungiyar hadin kai ta Shanghai ta jawo hankulan mutane sosai. Mun sami labari cewa, a cikin takardar, za a tabbatar da tunanin sada zumunta daga zuri'a zuwa zuri'a da kare zaman lafiya har abada a tsakanin jama'ar kasashen da ke cikin kungiyar hadin kai ta Shanghai bisa dokokin shari'a, wannan ne mataki daban mai muhimmanci ga tabbatar da zaman lafiya a shiyyar.

Mai ba da shawara ga ministan harkokin waje na kasar Sin Li Hui ya bayyana cewa, a duk tsawon lokacin taron koli, shugabannin za su waiwayi nasarorin da kungiyar ta samu bayan  kafuwarta da kuma tsara sabbin shirye-shiryen yin hadin guiwa da aiwatar da harkokin waje wajen tsaron kai da tattalin arziki da al'adun da ke dacewa da 'yan adam da kuma musanya ra'ayoyinsu a kan manyan batutuwan kasa da kasa da shiyya shiyya a fannoni da yawa.

Bayan taron, Shugabannin za su je duba rawar dajin da aka yi don yaki da ta'addanci, Mr Li Hui ya bayyana cewa, kasashen 6 da ke cikin kungiyar hadin kai ta Shanghai suna son kara zurfafa hadin guiwa da ma'amala a tsakaninsu wajen tsaron kai ta hanyar rawar dajin da kuma kara daga karfinsu na yaki da ta'addanci.

An bayyana cewa, ziyarar Hu Jintao za ta kara inganta huldar da ke tsakanin kasar Sin da sauran kasashen da ke makwabtaka da ita da kuma kara sanya zumunta a tsakaninsu.(Halima)