Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-14 15:18:54    
Babban tsaunin Aershan, muhimmin bangare ne na manyan tsaunukan Daxing'anling

cri

Babban tsaunin Aershan yana gabashin jihar Mongolia ta Gida mai cin gashin kanta, shi ne kuma bangare na tsakiya na babban tsaunukan Daxing'anling. Tsawonsa ya wuce kilomita dari 2. An mayar da shi tamkar koren lu'ulu'u na babban tsaunukan Daxing'anling a sakamakon bihiyoyi da ciyayi masu dimbin yawa da aka dasa a wajen. Tekun bishiyoyi da marmaron ruwa mai zafi da kankara da kankara mai taushi da filayen ciyayi da kuma wurin tarihi na duwatsu masu aman wuta da koguna da kuma tabkuna, dukkansu sun samar da wannan kyakkaywan wuri. Madam Chen Hongyuan, mai jagorancin masu yawon shakatawa domin yin ziyara a babban tsaunin Aershan, ta yi karin bayanin cewa,

'Cikakken sunan babban tsaunin Aershan shi ne babban tsaunin Halun'aershan. A bakin 'yan kabilar Mongolia, ma'anar Halun ita ce zafi, ma'anar Aershan kuwa ita ce ruwa mai tsarki. Shi ya sa babban tsaunin Aershan ya yi suna ne domin marmaron ruwa mai zafi da aka samu a nan, a maimakon wani shahararren bangarensa.'

To, da farko bari mu yi magana kan marmaron ruwa mai zafi a wajen. Marmaron ruwa mai zafi da aka samu a babban tsaunin Aershan, marmaron ruwa mai zafi ne da ba safai a kan ga irinsu a sauran wuraren duniya ba. Yawan idanun ruwa da suka bullo a yankuna 4 a nan ya kai 76.

Bisa binciken da hukumomin da abin ya shafa suka yi, an ce, marmaron ruwa mai zafi na babban tsaunin Aershan na kunshe da sinadarin tagulla da manganese da strontium da sauran kananan sinadari da kuma sinadarin radium da uranium da ke ba da iska mai guba, wadannan abubuwa na iya shawo kan cututtukan da ke shafar kayayyakin jikin mutane a fannonin motsa jiki da hadiye da zuciya. Musamman ma suna iya warka da ciwon murda da kafa a sakamakon amosanin kashi da amosanin gabbai da raunuka.

Dakin nune-nunen marmaron ruwa mai zafi na babban tsaunin Aershan wuri ne mafi girma da aka fi samun marmaron ruwa mai zafi a wurin yawon shakatawa na babban tsaunin Aershan. Marmaron ruwa mai zafi guda 37 suna cikin wannan dakin nune-nune mai fadin murabba'in mita 5700 ko fiye, ta haka dakin ya yi kama da wani gadinar rani. A gaban marmaron ruwa mafi zafi, malam Wang Bin mai jagorancin masu yawon shakatawa ya yi karin bayani kan amfanin ruwan, ya ce,

'Shi ne marmaron ruwa mafi zafi a dukkan marmaron ruwa mai zafi guda 37. Masu fama da ciwon gabbai ko kuma wadanda ke fama da matsalar tafiya suna iya kyautata jikunansu bayan da suka yi kwanaki 21 ko 22 suna amfani da ruwan.'

Marmaron ruwa mai zafi da aka samu a babban tsaunin Aershan ya jawo masu yawon shakatawa masu dimbin yawa daga wurare daban daban a gida har ma a ketare saboda amfanin musammansa na kiwon cututtuka. Madam Katusha 'yar kasar Rasha ta nuna babban yabo kan amfanin marmaron ruwan, ta ce,

'Na san wannan marmaron ruwa mai zafi daga sashen aikin yawon shakatawa na kamfanin kasuwancin man fetur na Manzhouli. Na zo nan bayan da na ketare hanya mai tsawon kilomita fiye da 200 daga kasar Rasha, amma duk da haka a karo na 5 ne na zo babban tsaunin Aershan. A idona, shan ruwan na da amfani, sa'an nan kuma, yin wanka a ruwan na taikawa mana sosai. Bayan da muka ya da labaru game da marmaron ruwan a tsakaninmu har tsawon shekaru 3 ko fiye, mutanen Rasha da suka zo nan ya fi mutanen Sin yawa.'

Baya ga marmaron ruwa mai zafi, wurin tarihin duwatsu masu aman wuta na Halaha da aka samu a babban tsaunin Aershan ya kuma jawo hankulan masu yawon shakatawa. Sun hade da duwatsu masu aman wuta na Haerqingeer da aka samu a kasar Mongolia, ta haka sun zama mashahuran manyan duwatsu masu aman wuta a kasar Sin. Tabkin Tianchi na daya daga cikin tabkuna da yawa da ke bakin duwatsu masu aman wuta na babban tsunin Aershan, yana kololuwar wani babban dutse mai tsayin mita 1300 ko fiye daga leburin teku.

Dalilan da suka sa tabkin Tianchi ya shahara a babban tsaunin Aershan su ne domin ba a iya kidayar zurfinsa ba, na biyu kuma, zurfinsa bai canza ba saboda ba shi da wurin shigo da ruwa, haka kuma ba shi da wurin fitar da ruwa. Na uku kuma, kifaye ba su iya rayuwa a cikin tabkin ba. Ban da wannan kuma, in an hange shi daga jirgin sama, ya yi kama da wani lu'ulu'u mai launin shudi da aka ajiye shi a kololuwar babban dutse.(Tasallah)