Masu bincike na kasashen Amurka da Spain sun yi shekaru 20 suna yin bincike kan 'yan kasar Amurka dubu dari 128, sakamakon da suka samu ya nuna cewa, shan kofi da yawa cikin dogon lokaci bai kara wa yawancin mutane barazanar kamuwa da ciwon zuciya ba.
An taba ba da sakamakon bincike a watan Maris na shekarar da muke ciki cewa, idan mutane suna da wasu kwayoyin halitta wato gene na musamman a cikin hanta, caffein ya narke sannu sannu, ta haka, shan kofi da yawa ya iya kara kawa wa wadannan mutane karazanar kamuwa da ciwon zuciya.
Amma wadannan masu bincike na kasashen Amurka da Spain sun gabatar da rahoto a ran 24 ga watan Mayu cewa, binciken da suka yi ya nuna a bayyane cewa, shan kofi da yawa ba zai kara barazanar kamuwar da ciwon zuciya ba. Ba su gano cewa, yawan kofi da shayi ko kuma kofi maras caffein da mutane suka sha ba ya da nasaba da kamuwa da ciwon zuciya ba. Masu bincike sun yi bincike ga mutane a fannonin abinci da motsa jiki na yau da kullum da sauran al'adun kiwon lafiya a lokaci-lokaci, sun kuma duba musu lafiya a lokaci-lokaci. Masu bincike sun bayyana cewa, sabon sakamako wani labari ne mai kyau, saboda kofi tana daya daga cikin abubuwan sha da suka fi barbazuwa a duniya. Amma sun yi nuni da cewa, ba a iya kawar da cewa, shan kofi zai haifar da ciwon zuciya ga wasu mutane ba.
Masu bincike sun jaddada cewa, sun yi bincike ne kan kofin da aka tace kawai, mai yiwuwa ne za a sami wani sakamako daban, in an yi bincike kan kofin da ba a tace ba ko kuma aka yi shi a cikin tukunyar tace kofi iri ta kasar Faransa.(Tasallah)
|